Gwamnan Niger zai gurfana a gaban Kuliya

Gwamnan Niger zai gurfana a gaban Kuliya

-Gwamnan jihar Niger, Abubakar Bello zai bayyana a gaban kotun zabe don ya bayar da shaida akan tuhumar da ake yi masa

-Dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP Umar Nasko na tuhumar gwamnan jihar da yin amfani da takardun bogi

-Lauyan gwamnan ya bayyana ma kotu cewa Abubakar ba wani abu da yake boyewa a sabida haka zai bayyana da kansa don ya bada shaida

Gwamnan jihar Niger, Alhaji Abubakar Sani Bello zai bayyana a gaban kotun zabe don ya bada shaida akan tuhumar da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a zaben 2019 ke yi masa akan cewa takardun bogi ke gareshi.

A zaman da akayi a ranar Alhamis 27 ga watan Yuni 2019, jagoran lauyoyin gwamna Bello, Jibrin Samuel Okutepa SAN, ya bayyana cewa wanda ya ke karewa zai bayyana gaban kotun don ya bayar da shaida.

Okutepa ya bayyana cewa mai tuhumar, dan takarar gwamna na PDP, Nasko, shi da jam’iyyar shi sun gabatar da shaida guda daya tal. Ya bayyana ma kotun cewa zai kira wanda yaker karewa, gwamna Abubakar Sani Bello a matsayin shaidarsa.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin Legas za ta gayyato Falana ya bada shaida akan Evans

Ya bayyana cewa wanda yake karewa bashi da wani abu da yake boyewa, a saboda haka zai bayyana a kotun don ya bayar da shaida.

Sakamakon rashin samun sammace daga kotu da zai tilastawa sauran shaidun mai kara su bayyana gaban kotun don su bayar da shaida, hakan ya sanya lauyan mai kara, barista Mohammed Ndayako ya kira shugaban jam’iyyar PDP barista Tanko Beji a matsayin shaidarsa.

Tun farko dai, shugaban jam’iyyar ya bayyana a gaban kotun inda ya tabbatar da shaidar da ya bada a rubuce sa’annan ya bukaci kotun da ta yi amfani da shaidar.

Ya bayyana takarda mai namba CF001 da Abubakar Bello da Ahmed Muhammed Ketso suka cika, kwalin digiri na jami’ar Maiduguri dauke da sunan Abubakar Sani Bello da aka bayar a ranar 23 ga watan Nuwamba 1993, takardar bautar kasa da aka bayar a ranar 1 ga watan Mayu 1993, katin jam’iyyar APC, takardar makarantar firamare da aka bayar a shekarar 2006 dauke da sunan Ahmed Mohammed Ketso da wasu takardun.

Lauyan wadanda ake tuhuma yayi jayayya akan karbar wadannan takardu a matsayin shaida a kotun, inda kuma yayi alkawarin zaiyi bayani akan takardun a lokacin da zasu yi jawabin karshe a kotun.

Alkalin ya dage sauraron kara zuwa zama na gaba inda wadanda ake tuhuma zasu fara gabatar da shaidunsu.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: