Jami'ar tarraya da ke Dutse ta dawo da dalibai 40 da ta kora bisa kuskure

Jami'ar tarraya da ke Dutse ta dawo da dalibai 40 da ta kora bisa kuskure

Jami'ar gwamnatin tarayya, Dutse (FUD) da ke jihar Jigawa, ta dawo da wasu dalibai 40 daga cikin dalibai 485 da ta kora bisa rashin mayar da hankali a kan karatunsu da wasu laifuka a zangon karatun da ya gabata.

Mataimakin shugaban jami'ar mai kula da harkokin karatu, Farfesa Abdulkarim Sabo, ya bayyana cewa jami'ar ta dawo da daliban ne bayan ta gano cewa ta tafka kuskure wajen korarsu. Ya ce jami'ar ta gano kuskuren ne bayan ta sake nazarin takardun dalilin korar daliban.

Jami'ar ce ta fara umartar daliban da ta kora da su aike da rubutaccen korafi a kan korar da aka yi musu idan suna da shi.

A ranar Alhamis ne jami'ar ta bayyana cewa ta dawo da wasu daga cikin daliban da ta kora bisa kuskuren alkalami.

"Ba za a kara samun irin wannan kuskuren ba, saboda yanzu jami'ar ta rungumi wasu dabarun fasahar zamani wajen tattara wa da adana bayanan daliban ta," a cewar Farfesan.

DUBA WANNAN: Tashin hankali: Wata mata ta kashe mijinta ta kuma cinna wa gawarsa wuta

Ya kara da cewa jami'ar ta samar da wasu dabarun koyar wa da suka saukaka mu'amala tsakanin malamai da dalibai.

Kazalika, jami'ar ta ce ta yaye dalibai 558 daga tsangayoyin karatu daban-daban; 14 daga cikin daliban sun fita da sakamakon wuce sa'a.

Shugabar jami'ar, Farfesa Fatima Batul-Mukhtar, ce ta sanar da hakan yayin bikin yaye daliban jami'ar a karo na hudu tun bayan kafa ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng