Kyawon tafiya dawowa: Neymar zai sake koma wa Barcelona

Kyawon tafiya dawowa: Neymar zai sake koma wa Barcelona

-Dan wasan gaban PSG da Brazil, Neymar na son komawa tsohon kulob dinsa wato Barcelona

-Mataimakin shugaban kungiyar Barcelona Cardoner ya tabbatar da wannan zance cewa hakika Neymar na son dawowa Barcelona

-Amma kuma a cewarsa, Barcelona bata tuntunbi kungiyar PSG kan batun dan wasan kasar Brazil din ba

Dan wasan gaban Paris St-Germain, Neymar na son ya sake komawa Camp Nou in ji mataimakin shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.

Sai dai kuma Jordi Cardoner ya ce ba su tuntubi juna da Neymar ba, wanda ya kwashe tsawon kaka hudu a Barcelona.

KARANTA WANNAN:Mijina baya haihuwa, wata mata ta shaidawa kotu

Dan wasan kasar Brazil, mai shekaru 27 bai samu sakin jiki ba a PSG tun komawarsa kasar Faransa, bayan da aka saye shi a matsayin dan wasa mafi tsada a duniya.

Neymar ya koma PSG daga Barcelona a shekarar 2017 kan kudi fam miliyan 200, a matsayin dan wasa na farko da ya fi kowa tsada a duniya.

Cardoner ya fadi a yayin ganawa da ‘yan jarida cewar, ana ta rade-radin inda Neymar zai koma da taka leda idan dan wasar ya zabi barin kungiyar PSG.

Sai dai ya kara da cewa, “ Akwai yiwu war Neymar na son komawa Barcelona” sai dai kuma Barca bata tunanin sake daukar dan wasan ko kuma na zama ta tattauna da PSG a kan batunsa.

Neymar ya samu nasarar lashe kofin Ligue 1 a PSG, inda ya zura kwallaye 34 a wasanni 36 da ya buga a Faransa.

Duk da haka, dan wasan na samun cikas a dakin sauya kayan ‘yan kwallo, inda ake rade-radin cewa ana yawan fada da shi. Bugu da kari, rahotanni daga Spaniya na cewa dan wasan ya bukaci a zabtare Yuro miliyan 12 a kudinsa na shekara domin ya samu komawa Barcelona.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng