Kotu ta dage sauraron karar da mahukuntan fadar Kano suka shigar kan Ganduje

Kotu ta dage sauraron karar da mahukuntan fadar Kano suka shigar kan Ganduje

- Kotu ta dage sauraron karar da mahukuntan fadar Kano suka shigar kan Gwamna Ganduje

- Mahukuntan dai na karar Ganduje tare da wasu bakwai kan kafa sabbin masarautu da kuma nada sabbin sarakuna a jihar

- Alkali mai sauraren karar, Justis Ahmed Tijjani Badamosi ya daga sauraran karan zuwa ranar 16 ga watan Yuli

Wata kotu da ke zama a Kano a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuni ta dage sauraron karar da mahukuntan fadar jihar suka shigar akan Gwamna Umar Ganduje da wasu mutane bakwai.

Mahukunta hudu na fadar Kano, Yusuf Nabahani (Madakin Kano), Abdullahi Sarki Ibrahim (Makaman Kano), Bello Abubakar (Sarkin Dawakin Mai tuta) da Muktar Adnan (Sarkin Mai Kano), sun shigar da karar Kakakin majalisar dokokin Kano, Gwamnan jihar Kano, Babban alkali , Tafida Abubakar Ila, Ibrahim A Gaya, Ibrahim Abubakar II da Aminu Ado Bayero bisa kafa sabbin masarautu da nada sarakuna.

Lauyan mai shigar da kara Lateef Fagbemi (SAN) da lauyan wanda ake tuhuma, Ibrahim Muktar sun amince da ranar 16 ga watan Yuli a matsayin ranar cigaba da sauraron karan

KU KARANTA KUMA: Kada wanda ya sake gayyatana taro idan har bai son na fallasa abunda ke raina – Sarkin Kano

Alkali mai sauraren karar, Justis Ahmed Tijjani Badamosi ya daga sauraran karan zuwa ranar 16 ga watan Yuli don cigaba da sauraran shari'ar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya kacaccala masarautun jihar zuwa yanka biyar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel