Kazanta da rashin kunya: Kotu ta raba auren Baraka da Ibrahim saboda

Kazanta da rashin kunya: Kotu ta raba auren Baraka da Ibrahim saboda

Wata kotu ta musamman da ke yankin Mapo a jihar Oyo ta raba auren da ke tsakanin Jimoh Ibrahim da matarsa, Barakat Ibrahim, saboda kazantar tsiya da muguwar rashin kunyar Baraka.

Baya ga hakan, kotu ta warware auren ne bayan ta gano cewar Ibrahim da Barakat sun daina kaunar juna.

Ademola Odunade, alkalin kotun, ya bawa Barakat damar cigaba da rikon da daya tilo da suka haifa mai shekaru 8 a duniya, sannan ya umarci Ibrahim da ya dauki nauyin karatun yaron da kuma biyan kudi N5,000 duk wata domin ciyar da yaron.

Ibrahim, mazaunin Oja-Oba a garin Ibadan, ya garzaya gaban kotun domin neman a raba aurensa da Barakat saboda tsabar kazanta da rashin da'a da ta ke nuna masa.

Ya shaida wa kotun cewar Barakat na yawon karuwanci da bin samari har kasashen ketare domin su hole.

"Na yi hakuri sosai da Barakat a tsawon shekaru 11 da muka yi tare bisa tunanin cewa wataran za ta canja halayenta. Ni ne ke share gida, na yi wanke-wanke amma duk da haka idan ta dawo daga yawon ta na banza sai ci min mutunci," a cewar Ibrahim.

A nata bangaren, Barakat bata musanta korafe-korafen Ibrahim ba, sannan ta amince da bukatarsa na a warware aurensu.

A cewar Barakat, wannan ba shine karo na farko da Ibrahim ya nemi a raba aurensu ba. Ta shaida wa kotun cewar ta gaji da bin Ibrahim har gida domin ta bashi hakuri duk lokacin da suka samu sabani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel