Farin jinin da nake dashi a gurin mata yasa abokaina suka yi mini wani mugun kazafi - Inji Bello

Farin jinin da nake dashi a gurin mata yasa abokaina suka yi mini wani mugun kazafi - Inji Bello

Matashin da jami’an yan sanda jihar Jigawa suka kama, Muhammad Bello wanda ake zargi da kasancewa babban dan fashi da makami ya karyata zargin da ake masa.

Bello ya bayyana cewa abokan sa ne ke bakin ciki da ganin kyashin sa, har suka hada baki da ’yan sanda aka kama shi.

A cewarsa abokan sa na bakin ciki da shi ne saboda ya na da farin jini wajen ’yan mata, kowace sai tace shi ta ke so.

Wanda ake zargin ya ce abokan sa suka shirya masa tuggun sharrin fashi domin kawai ‘yan sanda su kama shi.

A ranar Talta, 25 ga watan Yuni ne yan sanda suka kama shi. An kama shi a Zaria a lokacin da ya ke gudun buya. Dama kuma sunan sa na daga cikin manyan rikakkun ’yan fashin da ake nema a jihar Jigawa.

Sai dai kuma ya ce farin jinin da ya ke da shi a wajen mata ne ya janyo masa shiga cikin wannan musifa.

KU KARANTA KUMA: An saka wa El-Zakzaky guba, mu na da hujja - Mabiya Shi'a

Yace: “Duk kasuwar da na shiga ko garin da na je, sai ’yan mata su yi ta nuna min so, ko da kuma su na tare da samarin su ne. sau da yawa ma su ke fara yi min magana ko da ni ban yi musu ba.”

“Dalilin da ya sa kenan wasu abokai na da ke yankin mu masu kishi saboda ina kashe musu kasuwar-’yan mata kuma su na jin haushin irin rayuwa ta suka ce wa ‘yan sanda wai ni dan fashi da makami ne.

“Amma babu wani abu, kawai don ’yan mata sun fi so na ne a kan su,” cewar Bello.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel