Sai na bawa mata ta cin hanci kafin ta amince da ni - Miji ya koka a gaban kotu

Sai na bawa mata ta cin hanci kafin ta amince da ni - Miji ya koka a gaban kotu

Wani limamin Coci, Abayomi Adeboyega, mai shekaru 48, ya garzaya kotu domin neman a raba aurensa da matar sa bayan sun yi zama tare na tsawon shekara 16.

Mista Adeboyega ya shaida wa wata kotu ta musamma da ke Igando a jihar Legas cewa ya na so a raba aurensa da matarsa, Risikat, saboda ta na hana shi ya sadu da ita duk lokacin da bai ba ta cin hancin kudi ba.

"Mata ta na bari na da yunwar jima'i, ba ta bari na kwanta da ita matukar ban ba ta kudi ko kyautar wani abu ba," a cewar sa.

Ya ce zai kashe kansa matukar kotun ba ta raba aurensa da Risikat ba duk da sun haifi yara har hudu tare.

"Ba na bukatar Risikat a kusa da ni, ba na bukatar duk wani abu da zai kara hada ni da ita.

"Ta na bata min rai, zan kashe kai na idan kotu ba ta raba wannan aure da babu soyayya a cikinsa ba," Adeboyega ya fada wa kotun.

Kazalika, ya sanar da kotun cewa matarsa ba ta dafa masa abinci sai a kurarren lokaci, sannan ta na yawo ta na bata masa suna a gari.

"Mata ta na son Coci na ta durkushe, saboda ta na yawo ta na bata min suna a wurin mabiya na da kuma mutanen da ke zuwa neman taimako a wuri na. Yanzu ga shi jama'a sai gudu na suke yi," Adeboyega ya fada wa kotu.

Sannan ya kara da cewa Risikat na yin fada da masu zuwa Cocinsa.

Saidai, Risikat, mai shekaru 39, ta musanta dukkan zargin da mijinta ya ke yi mata tare da bayyana cewar shine ke yi wa rayuwar ta barazana da tsibbun da ya ke yi.

Amma duk da hakan, Risikat ta roki kotun da kar ta raba aurenta da mijinta saboda har yanzu ta na son sa a haka duk da matsalolinsa.

Alkalin kotun, Adeniyi Koledoye, ya bukaci ma'auratan su zauna lafiya da juna albarkacin yaran da suka haifa tare.

Ya daga sauraron karar zuwa ranar 11 ga watan Yuli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel