Kwadayi mabudin wahala: Yawancin 'yan mata na soyayya ne saboda neman abin sakawa a bakin salatin su - Bincike

Kwadayi mabudin wahala: Yawancin 'yan mata na soyayya ne saboda neman abin sakawa a bakin salatin su - Bincike

- Wasu masan masu bincike a fannin soyayya sun gano wani muhimmin abu dangane da masoya na wannan zamani

- Masanan sun gano cewa da yawa daga cikin 'yan mata suna soyayya ne saboda suna son samun dan abinda zasu sanya a bakin salatin su

- Bayan haka masanan sun bayyana cewa da yawa daga cikin matan da suke hawa yanar gizo suna hawa ne kawai domin samun samari na soyayya

Wasu kwararrun likitoci a bangaren sanya ido akan halayen dan adam dake jami'o'in Azusa Pacifi da kuma UC Merced dake kasar Amurka sun binciko cewa duk mace guda daya daga cikin mata uku na yin soyayya ne saboda dan abinda za su samu su sanya a bakin salatin su da kuma dan abinda za su kashe.

Sakamakon binciken ya bayyana cewa kusan kashi 23 zuwa 33 cikin 100 na matan da ke hawa shafukan sada zumunta na yanar gizo suna hawa ne saboda ko wani saurayi zai taya ya ce yana so.

Sanna kuma binciken ya gano cewa, irin wadannan 'yan mata sukan fada soyayya ne da namiji idan suka fuskanci cewa yana da abin hannu, ma'ana kudi.

KU KARANTA: Wata kila Aljanu ne suka jefawa Atiku ruwan kuri'u ba mutane ba - Mutane

Jennifer Howell, Brian Collison da Trista Harig sune suka yi wannan bincike.

Yawan 'yan matan da suke soyayya da mata jinsinsu sun kai kimanin 820, sannan kuma da yawan su dama yawon banza suke yi a yanar gizo babu wanda ya taya, balle yace yana so.

A wani bangaren kuma an samu kimanin mata da suke soyayya da maza zalla da suka kai kimanin 357.

A karshe dai sakamakon binciken ya nuna cewa maza da mata da yawa sun bayyana cewa ba su ga wani laifi dan mutum ya fada tsundum cikin soyayya ba don zai samu wani abu a hannun masoyinsa.

Sai dai a wajen irin wadannan masoyan duk soyayyar da ba za a amfana da juna ba, to ba jimawa take yi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel