An kuma: Amarya ta yiwa mijinta allura da fiya-fiya jim kadan bayan bikinsu

An kuma: Amarya ta yiwa mijinta allura da fiya-fiya jim kadan bayan bikinsu

- Kwana kadan bayan abinda ya faru tsakanin mata da miji a jihar Kano, inda matar taa dauki wuka ta cakawa mijinta

- Yanzu haka dai an sake kwata wani abu makamancin haka, inda ita kuma wannan tayi amfani da maganin fiya-fiya ta yiwa mijinta allura ba jimawa da yin aurensu

- Rahotanni sun nuna cewa matar tayi hakanne bayan kawayenta sun zuga ta akan cewa ta kashe shi ta koma Abuja za su hada ta wani mutumi mai kudi

Ana zargin wata sabuwar Amarya da yiwa mijinta allura da maganin bera na fiya-fiya a jihar Kaduna.

Wani mai amfani da shafin sada zumunta na Facebook, Mansur Salihu, wanda ya wallafa labarin a shafinsa, ya bayyana cewa wasu abokanan matar ne suka bata gurguwar shawara akan ta kashe mijinta za su hada ta da wani mutumi mai kudi a Abuja.

KU KARANTA: Ikon Allah: Labarin wani gari da mata ke juyewa su zama maza idan suka tashi balaga

Ga abinda mutumin ya rubuta a shafinsa na Facebook:

"Wata sabuwar amarya ta yiwa mijinta allura da fiya-fiya, bayan kawayenta sun bata gurguwar shawarar ta kashe mijin nata domin ta koma Abuja za su hada ta wani mutumi mai kudi.

"Yanzu haka mijin yana asibitin koyarwa na Jos yana karbar magaani. Allah ya kyauta," in ji Mansur Salihu.

Satin da ya gabata ne wata mata ta dauki wuka ta cakawa mijinta, bayan wata bakwai da yin auren, inda aka yi gaggawar garzayawa da shi asibiti. Sai dai matar ta bayyana cewa ta yi hakan ne domin ta kare kanta, inda ta bayyana cewa babu abinda mijin nata ya iya idan ba ya dinga dukanta ba, bayan kuma tana dauke da ciki na wata hudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel