Ikon Allah: Labarin wani gari da mata ke juyewa su zama maza idan suka tashi balaga

Ikon Allah: Labarin wani gari da mata ke juyewa su zama maza idan suka tashi balaga

- Wani abin al'ajabi da yake faruwa a tsibirin Salinas, yana jawo hankalin mutane da dama

- Yayin da mata kanana ke juyawa su zama maza a lokacin da suka kai minzalin balaga

- Masana sun sanar da cewar hakan na faruwa ne saboda rashin isasshiyar wata kwayar halitta a jikin matan lokacin da suke yara

Akwai wani abu mai daure kai da ban mamaki game da yanayin mutanen kauyen Salinas dake yankin Caribean, wanda ya zama abin kwatance ga al'umma.

Abu ne wanda kowa ya sani cewa yara mata da aka haifa a tsibirin suna komawa maza, yayin da mazakuta ke fito musu a gabansu a lokacin da suka tashi balaga.

Ana samun daya daga cikin yara 90 da aka haifa a kauyen, ya juya ya zama namiji a lokacin da suka kai shekaru 12 a duniya.

KU KARANTA: Tirkashi: Fatima Ganduje ta mayar da martani ga masu zagin mahaifinta

Masana a fannin kimiyya sun bayyana cewa yaran suna juyawa ne zuwa hallitar namiji saboda sun rasa wani sinadari a jikinsu wanda yake karesu daga juyawa zuwa maza.

Duka jarirai tun suna cikin mahaifiyarsu, suna da kwayar halitta a jikinsu da ake kira da 'Gonads' a turance da kuma wani abu da ake kira 'Tubercle' a tsakanin kafafunsu.

A lokacin da suka cika sati 8 a cikin mahaifiyarsu, wadanda suke maza wannan kwayoyin halittar suna juyawa su zama mazakuta, haka suma mata na su yana juyawa ya zama na mata.

Akwai kuma mazan da nasu kwayar halittar ba ta da tsawo sosai, sai a haifesu tamkar mace, a lokacin da suka kai minzalin balaga sai wannan kwayar halittar ya fito ya girma ya koma mazakuta, daga nan kuma muryar su da komai na su zai canja ya zama na namiji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel