AFCON 2019: Daya daga cikin 'yan wasan Najeriya ya yanke ciki ya fadi yayin atisaye a Masar

AFCON 2019: Daya daga cikin 'yan wasan Najeriya ya yanke ciki ya fadi yayin atisaye a Masar

- Samuel Kalu, daya daga cikin 'yan wasan kwallon Najeriya ya yanke jiki ya fadi yayin atisaye a ranar Juma'a

- Dan wasan yana motsa jiki ne a yayin da lamarin ya faru

- An garzaya da Kalu asibiti nan take inda aka ce ya yawaita shan ruwa da sauran ababen sha

Dan wasan Super Eagles, Samuel Kalu ya yanke ciki ya fadi a ranar Juma'a yayin da tawagar 'yan wasan ke atisaye domin tunkarar tawagar kasar Burundi a wasarsu ta farko a gasan cin kofin Afirka (AFCON).

Rahotanni sun ce dan wasan na kungiyar Bordeaux yana koyan bugun corner kick ne a lokacin da ya yanke jiki ya fadi.

Sai dai daga bisani rahotanni daga sansanin 'yan wasan ta Najeriya sun ce an garzaya da shi asibiti kuma ya dawo cikin hayacinsa.

DUBA WANNAN: Da duminsa: An kama kwararen mayaki na kasa da kasa cikin 'yan Boko Haram a Borno

Goal.com ta ruwaito cewa shugaban sashin yada labarai na kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Cif Demola Olajire ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya kara da cewa likitoci sun shawarci Kalu ya yawaita shan ruwa.

DUBA WANNAN:

"An sanar da ni cewa Samuel Kalu ya dawo hayyacinsa. An kai shi asibiiti domin yi masa gwaje-gwaje kuma an ce yanzu ya yi lafiya. Tsananin kishin ruwa ne ya sanya ya fadi. An fada masa ya yawaita shan ruwa," inji Olaajire.

Samuel Kalu ya buga wa Super Eagles wasanni biyar tun da ya fara buga mata wasa a 2018 kuma yana da kwallo daya a raga.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164