Rikicin siyasar Kaduna: El-Rufai na cikin tsaka mai wuya, yayin da jam'iyyar PDP ta nufi kotun daukaka kara

Rikicin siyasar Kaduna: El-Rufai na cikin tsaka mai wuya, yayin da jam'iyyar PDP ta nufi kotun daukaka kara

- A ranar 27 ga watan Yuni kotun daukaka kara ta jihar Kaduna, za ta saurari karar da jam'iyyar PDP ta kai mata ranar 9 ga watan Maris akan sake kirga kuri'u

- Kotun sauraron kararrakin zabe tace baza ta yarda da bukatar jam'iyyar na kirga kuri'u ba

- Jam'iyyar PDP ta ce za tayi iya yinta wurin ganin kotun daukaka kara tayi na'am da bukatar ta

Kotun daukaka kara ta jihar Kaduna ta ce ta sanya ranar Alhamis 27 ga watan Yuni a matsayin ranar da za ta saurari karar da babbar jam'iyyar adawa ta PDP ya kai mata, inda ta bukaci kotun ta bada umarnin sake kirga kuri'u, karar da ta kai ranar 9 ga watan Maris.

Lauyan dake jagorantar karar jam'iyyar PDP, Elisha Kurah (SAN), da kuma dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar PDP, Isa Ashiru, sune suka bayyana hakan jiya Alhamis 20 ga watan Yuni, jim kadan bayan sun kammala wani taro akan zaben gwamnan jihar da aka yi.

Legit.ng ta gano cewa kotun sauraron kararrakin zabe ta yi watsi da bukatar jam'iyyar ta PDP akan bata damar sake kirga kuri'u a ranar 28 ga watan Mayu.

Wanda yake jagorantar sauraron kararrakin, mai shari'a Ibrahim Bako, ya ce kotun sauraron kararrakin tana da kwanaki 180 ne kawai kafin ta kammala sauraron karar.

Bako ya bayyana cewa ba zasu yarda da bukatar jam'iyyar ba ta neman sake kirga kuri'u ba.

KU KARANTA: Babbar magana: Mazan da auren mata masu kiba sun fi farin ciki da jimawa a duniya - Masana

Haka kumaa yaki amincewa da bukatar jam'iyyar na cewa a barta ta kirga kuri'un kananan hukumomi 12 kawai.

A ranar 25 ga watan Mayu ne jam'iyyar PDP da dan takarar ta Isa Ashiru, suka bukaci kotun sauraron kararrakin zaben da ta basu damar kirga kuri'un kananan hukumomin, Kaduna North, Kaduna South, Igabi, Birnin Gwari, Giwa, Zaria, Sabon Gari, Makarfi, Kudan, Kubau, Soba da karamar hukumar Ikara, wanda duk kusan jam'iyyar APC ce ta lashe su.

Bayan haka, Kurah ya ce jam'iyyar za ta nufi kotun daukaka kara ranar 27 ga watan Yuni domin kai kukanta.

Jam'iyyar ta ce za ta yi iya bakin kokarinta wurin ganin kotun daukaka karar ta aminta da bukatar ta.

Idan ba a manta ba Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Isah Ashiru, dan takarar gwamnan jam'iyyar PDP na jihar Kaduna a shekarar 2019, ya kai bukatar shi zuwa kotu akan ta bawa jam'iyyar PDP damar sake kirga kuri'u.

Ashiru wanda ya sha kasa a hannun gwamnan jihar Malam Nasir Ahmed El-Rufai, ya bukaci hakan ne a wata takarda da ya aikawa kotun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel