Babbar magana: Mazan da auren mata masu kiba sun fi farin ciki da jimawa a duniya - Masana

Babbar magana: Mazan da auren mata masu kiba sun fi farin ciki da jimawa a duniya - Masana

- A lokuta da dama, mata masu kiba ana yi musu wani kallo na daban, saboda yanayin girman jikinsu da kuma yadda siffarsu take.

- Bincike ya bayyana mata masu kiba sun fi iya soyayya, kuma suna taimakawa mazajen su matuka a dukkanin abubuwa na rayuwa

- Sannan mata masu kiba sun iya kwantarwa da mazajen su hankali, sannan kuma basu da zurfin ciki da boye-boye, hakan ne yasa zama dasu yake da matukar dadi fiye da sirara

Wani bincike da masana suka yi, ya bayyana cewa mazan da suke auren mata masu kiba sun fi farin ciki da kuzari, akan mazan da suke auren mata sirara.

Binciken wanda wani kwararren masani mai suna Dr. Filemon Alvarado da kuma Dr. Edgardo Morales na Jami'ar kasar Mexico suka yi, ya bayyana cewa mata masu kiba basu da zurfin ciki, kuma basa boye-boye akan abubuwa na dangane da rayuwarsu, hakan ne ya sanya soyayya dasu take da dadi matuka.

Binciken ya nuna cewa, matan masu kiba suna sanya mazajen su farin ciki fiye sau 10 fiye da wadanda suke auren sirara.

Na biyu shine, mata masu kiba suna da wata ni'ima wadda sai wanda ya aura zai gane.

KU KARANTA: Tirkashi: Dumu-dumu na iske mahaifiyata na zina da limamin mu a cikin gidanmu - Wata budurwa ta koka

Na uku kuma binciken ya nuna cewa, mata masu kiba suna murmushi tare da kwantarwa da mazajen su hankali fiye da da sirara, sannan kuma sun fi siraran mata taimakawa wajen neman mafita idan an shiga matsala.

Na karshe shine, mata masu kiba ana samun su wurin taimakawa mazajensu akan duk wata bukata tasu, hakan yasa zama dasu yake da dadi matuka.

Binciken ya gano cewa mata sirara, suna da zurfin ciki, kuma basu da dadin zama sannan basu iya soyayya ba, hakan yasa zama dasu yake zama tashin hankali.

A karshen binciken, masu binciken sun bayyana cewa mazajen da suka auri mata masu kiba sun fi jimawa a duniya, kuma sunfi yin rayuwa cikin farin ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel