Masana sun fadi dalilin da yasa tattalin arzikin Najeriya ba ya habaka

Masana sun fadi dalilin da yasa tattalin arzikin Najeriya ba ya habaka

Moody Investors Services, wani kamfani da ke kula da harkokin bayar da bashin kudi domin inganta tattalin arziki, ya bayyana dalilin da yasa tattalin arzikin Najeriya ya kasa hawa hanya dodar da za ta saka ya samu habaka kamar yadda ya kamata.

Kamfanin ya bayyana cewar duk da cewar tattalin arzikin Najeriya ya samu karu wa da da kaso 1.1% a shekarar 2018 idan aka kwatanta da habakar da ya samu a shekarar 2017, mataimakin shugaban kamfanin, Aurelien Mali, ya ce: "wannan karu war da tattalin arzikin ya samu bai isa ya kawo canji a rayuwar 'yan Najeriya ba."

Mali ya bayyana cewa, rauni ta bangaren harajin da gwamnati ke samu ne babban kalubalen da tattalin arzikin Najeriya ke fuskanta.

A wani taro da kamfanin ya gudanar a Legas, Mali ya bayyana cewa tsare-tsaren gwamnati a bangaren tattalin arziki sun kara tauye habakar da tattalin arzikin da ya kamata ya samu.

DUBA WANNAN: Zabe: Ba zan taba yafe wa INEC ba - Oshiomhole

"Rauni ta fuskar manufofin gwamnatoci, yawaitar samun matsalar cin hanci da jinkiri wajen kaddamar da muhimman canje-canje sun taka rawa wajen dakushe kaifin da ya kamata tattalin arzikin Najeriya ya kasance yana da shi," a cewar Mali

Mali ya kara da cewa: "duk da ana samun ingantuwar wasu tsare-tsaren da zasu bunkasa tattalin arziki, akwai matsaloli ta fuskar yadda ake gudanar kasafin kudi a matakin tarayya, jihohi da kananan hukumomi wadanda suka jawo wa tattalin arziki yin tafiyar wahainiya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel