Mayakan Boko Haram sun kai hari sansanan dakaru 4 a mako daya kacal

Mayakan Boko Haram sun kai hari sansanan dakaru 4 a mako daya kacal

A halin yanzu dai masana da masu sharhi na ci gaba da ikirarin cewa babu wata mahanga ta ganin karshen kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram a nan kurkusa a sakamakon yadda ta'addancin ta yaki ci yaki cinye wa.

A tsakanin ranar Laraba ta makon da ya gabata zuwa Talata ta wannan mako da muke ciki, kungiyar mayakan Boko Haram tare da hadin gwiwar mafi munin kungiyar ta'adda a doron kasa ta IS, ta kai wasu munanan hare-hare a kan wasu sansanan dakaru hudu na kasar Najeriya.

Wannan lamari na ci gaba da ciwa dakaru tuwo a kwarya tare da jefa zukatan su cikin fargaba musamman masu yaki da ta'addanci a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan Operation Lafiya Dole.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito a ranar Laraba 19, ga watan Yunin 2019, hare-haren kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram ya salwantar da rayukan dakarun soji da dama a sansanan Mobbar, Damasak, Monguno da kuma Gajirama a yankunan jihar Borno.

Kakakin rundunar sojin kasa na Najeriya, Kanal Sagir Musa, yayin ganawa da manema labarai ya ce kawo wa yanzu babu tabbacin adadin rayukan dakaru da suka salwanta a sakamakon wannan munanan hare-hare.

Baya ga salwantar rayukan dakaru, an yi asarar makaman dakaru na kimanin Naira miliyan ashirin da 'yan ta'adda suka yi awon gaba dasu yayin cin karen su babu babbaka.

A yayin da ake tsaka da gudanar da bikin dimokuradiya cikin fadin kasar nan a ranar 12 ga watan Yuni, 'yan ta'adda na Boko Haram sun kai hari sansanin dakarun soji dake kauyen Kareto a karkashin karamar hukumar Mobbar ta jihar Borno.

A ranar Asabar 15 ga watan Yuni, mayakan Boko Haram sun kai hari kan wani sansanin dakaru a garin Damasak na jihar Borno, inda sojoji da dama suka jikkata yayin da rayukan wasun su suka salwanta.

KARANTA KUMA: Kiwon Lafiya: Amfani 9 na Aya a jikin dan Adam

Rayukan dakarun soji biyar sun salwanta yayin da mayakan Boko Haram suka kai hari sansanin dakaru dake cikin karamar hukumar Monguno da misalin karfe 5.00 na Yammacin ranar Litinin 17, ga watan Yuni.

A halin yanzu dai kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram na ci gaba da cin karen ta babu babbaka wasu kasashen Afirka dake iyaka da gabar Najeriya a yankin ta na Arewa maso Gabas tun yayin da ta daura damarar ta'addanci tsawon fiye da shekaru goma.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel