An bayyana kason kwamishinonin Ganduje da za su koma zango na biyu

An bayyana kason kwamishinonin Ganduje da za su koma zango na biyu

Kashi 40 cikin 100 na kwamishinonin Kano ne za su koma kan kujerun su a zango na biyu na mulkin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje inji jaridar Daily Trust.

Wani majiya na kusa na gwamnan da ya nemi a sakayya sunansa ya shaidawa Daily Trust cewa kashi 60 cikin 100 na tsaffin kwamishinonin jihar ba za su sake komawa kan mukammansu ba a mulkin gwamnan zango na biyu.

A cewar majiyar, za ayi watsi da mafi yawancin kwamishinonin saboda ba su tabbuka wani abin azo a gani ba a zangon farko na Gwamna Ganduje.

DUBA WANNAN: Sarki Sanusi ya yi wa 'Yan Majalisar Dokokin Kano nasiha mai ratsa zuciya

Ya ce, "A halin yanzu, mutane 100 ne neman kujerar kwamishina. Wadannan mutane ne daga bangarorin tayuwa daban-daban. Wasu sun magoya bayan tsohon gwamna Shekarau ne, wasu kuma na hannun daman tsohon mataimakin gwamna, Hafiz Abubakar da 'yan bangaren Kwamishinan Kasa da Sifiyo, Architect Aminu Dabo."

Sai dai a halin yanzu gwamnan yana nazari sosai ne kafin ya zabi sabbin kwamishinonin inda ya ce gwamnan ya saka sabbin matakai na zaben sabbin kwamishinonin.

"Gwamnan ya ce a yanzu za a zabi kwamishinoni ne bisa yanayin ayyukan da su kayi a baya, biyaya ga jam'iyya, jajircewa wurin aiki, sanin makamashin aiki da hazakar kwakwalwa.

"Duk wani mai neman kwamishina da bai cika wadannan ka'idojin ba ba zai samu ba a wannan karon saboda gwamnan ya sha alwashin zaben mutane masu nagarta sosai ne da zai yi aiki tare da su," inji majiyar.

Majiyar ya kuma kara da cewa wannan karon gwamnan zai bayar da muhimmanci ga mata wurin nada kwamishinoninsa.

Ya ce nadin mata 11 a matsayin Farmanen Sakatare da gwamnan ya yi cikin 'yan kwanakin nan alalma ce da ke nuna ba za bar mata a baya ba wannan karon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel