Kiwon Lafiya: Amfani 9 na Aya a jikin dan Adam

Kiwon Lafiya: Amfani 9 na Aya a jikin dan Adam

Kasancewar ta a bar marmari da ak sarrafawa ta wasu hanyoyi daban daban wajen amfani, Aya wadda a turance ake kira da Tiger nuts ko kuma Ofio a yaren Yarbanci, ta kunshi sunadarai masu gina jiki da inganta lafiyar bil adama.

Baya ga gardin gaske yayin tauna a baka ko kuma kwankwadar ruwan ta mafi shahara da Kunun Aya a Arewacin Najeriya, Aya ta kunshi sunadarai masu bunkasa lafiya da kuma garkuwa wajen yakar wasu cututtuka da ka iya samuwa a jikin bil Adama.

A bushe ko kuma yayin da take 'danya, Aya ta kunshi sunadarai kamar su Phosphorus, Oleic acid, Potassium, Vitamin E da kumaVitamin C.

A sakamakon sunadarin narkakken Glucose da kuma sunadarin Fibre da babu shakka ya dara na Karas da kuma Kabeji wanda Aya ta kunsa, tana taka rawar gani wajen rage nauyin jiki, sa cin abinci tare da kariya ga cutar bugun zuciya, kwarnafi da tashin zuciya, cutar daji da kuma bunkasa kewayen jini a jikin dan Adam.

Tamkar 'ya'yan Zaitun, Aya ta kunshi sunadarin Lipids da kuma Magnesium gwargwardon yadda jikin bil Adama yake bukata a kowane yini da ya sanya take taka rawa wajen bunkasa lafiyar zuciya.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya gana da gwamnan Legas kan tashoshin ruwa

Aya ta kunshi sunadarin amino acid arginine dake taimakawa jiki wajen samar da sunadarin nitric oxide dake bayar da kariya ta cutar hawan jini. Hakan take wajen bayar da kariya ga cutar ciwon suga a sakamakon arzikin sunadarin Fibre da Aya ta kunsa.

Sunadarin Vitamin E na taimakawa kamfanonin sarrafa kayan kwalliya na mata wajen inganta lafiyar fata musamman wajen hana tamushewar fata da kuma hana bayyanar tsufa da wuri. Kazalika sunadarin Vitamin E na taka taimako kwarai da aniyya wajen inganta kuzarin iyali walau Mace ko na Namiji.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng