Mangal zai gina kamfanin sarrafa shinkafa na Naira biliya 15 a Katsina

Mangal zai gina kamfanin sarrafa shinkafa na Naira biliya 15 a Katsina

-Shugaban kamfanin sufurin jiragen sama na MAX, Dahiru Mangal, zai gina kamfanin sarrafa shinkafa na Naira biliyan 15 a Katsina

-Babban daraktan kamfanin, Fahad Mangal ya ce kamfanin zai rinka fitar da tan 300,000 na shinkafa a duk rana

-Babban daraktan ya kara da cewa idan aka gama gina kamfanin, za a samar da aiki a kalla 10,000

A ranar Lahadin da ta gabata ne, gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya kaddamar da assasa ginin kamfanin sarrafa shinkafa mai suna Darma Rice Mill, mallakin shugaban kamfanin sufurin jiragen sama na Max kuma shugaban kamfanin gine gine na AFDIN, Alhaji Dahiru Mangal, wanda za a gina akan kudi Naira biliyan 15.

Gwamnan, ya ce dole a yaba da aikin wanda ana tsammanin zai samar da ayyukan yi fiye da 10,000 idan aka gamashi.

Masari ya ce yana da mahimmaci, yan kasuwa masu zaman kansu su taimaka wa gwamnatin wajen ganin an karfafa tattalin arzikin kasa ta hanyar zuba hannun jari wanda zai samar da ayyukan yi sa’annan ya ciyar da harkar kasuwanci gaba.

“Mangal ya ansa kiran shugaban kasa na cewa mutane su koma gona, noma shine rayuwarmu kuma shine komai namu.

“Duk wanda yake irin wannan aikin to yanayin sadaukarwa ce, Allah ne kadai yasan yawan mutanen da za su amfana da wannan aiki.

“Sai mu roki Allah da ya bashi ikon kammala wannan aiki.” A cewarshi.

Gwamnan ya kara da cewa gwamnati zata tallafa ma dukkanin ayyukan cigaba da zasu taimakama jihar ta ci gaba.

KARANTA WANNAN: Barayi ne suka sace N6.90m a gidan Zoo na Kano ba gwaggon biri ba – Manajan Darakta

A jawabin babban daraktan kamfanin, Fahad Mangal, ya ce idan aka gama aikin, kamfanin zai rinka sarrafa shinkafa tan 300,000 a duk shekara.

“Kamfanin zai sarrafa tan 16 a kowanne sa’a daya, zai rinka fitar da layuka biyu kowane akan tan 150,000 a shekara, kowanne layi zai kasance yana da hanyarsa ta wutar lantarki mai karfin 2MW.”

Ya kara da cewa aikin an rabashi gida biyu ne, kuma za a gamashi a cikin wata hudun farko na shekarar 2020.

A cewarshi, aikin zai taimakawa kasa wajen ganin an sami isasshiyar shinkafa don amfanin cikin gida kuma a kai matakin da ake so na samar da shinkafa.

Ya kara da cewa aikin zai kuma rage talaucin da ake fama dashi. Ya ce ”Idan aka kaddamar da aikin, kamfanin shinkafar sai samar da aiki a kalla 10,000 a jihar, wanda hakan zai taimaka kwarai wajen habbaka tattalin arzikin jihar ya kuma samar da kananan manoma.

Babban daraktan ya kara da cewa kwanan nan zasu kaddamar da kamfanin samar da takin zamani mai suna ‘Gobarau Agro Allied Feritilizers Blending Plant’ wanda zai ci kudi Naira biliyan 1.5

Ya bayyana cewa ayyukan zasu ciyar da jihar gaba sosai kuma zasu habbaka ayyukan noma a kasa baki daya.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel