Magani a gonar yaro: Magunguna 18 da Zogale ke yi a jikin Dan Adam

Magani a gonar yaro: Magunguna 18 da Zogale ke yi a jikin Dan Adam

- Daya daga cikin ganyen da ke da mutukar amfani a jikin mutum shine ganyen zogale

- Zogale abu ne da ake samun shi a gurare da dama, ciki hadda gonaki da gidajen mutane, saboda bashi da wahalar fitowa

Akwai ganye da 'ya'yan itatuwa da masana na gargajiya dana kimiyya suka gabatar da bincike akan su, wanda suka nuna cewa suna da matukar amfani a jikin dan adam, wasu kuma suna yin maganin cututtuka da dama a jikin mutum.

Mun yi kokarin kawo muku magunguna guda goma sha takwas da zogale ke yi a jikin dan adam. Ga sunan mun jero muku a kasa:

1. Ana amfani da garin ganyen zogale akan rauni ko gembo domin samun waraka.

2. Ana hada garin ganyen zogale da man zaitun a dinga shafawa a jiki, yana maganin kurajen jiki.

3. Ana shafa danyen ganyen zogale akan rauni domin samun waraka.

4. Ana shafa ganyen zogale akan goshi domin maganin ciwon kai.

5. Ana dafa ganyen zogale da zuma a dinga sha kamar shayi domin maganin Olsa (Ulcer).

6. Wanda yake yawan yin fitsari ma'ana cutar suga, ya rinka jika furen zogale da citta ya dinga sha kamar shayi.

7. Mace mai shayarwa za ta iya amfani da furen zogale da zuma ta dafa domin samun ruwan nono isasshe.

8. Ana amfani da ruwan danyen zogale, ga masu ciwon ido ko kunne, zasu diga a kunne ko ido.

9. Ana amfani ganyen zogale da kanwa 'yar kadan a dinga sha domin maganin shawara.

KU KARANTA: Ikon Allah sai kallo: Wata mata ta haihuwa bayan shafe shekaru 10 dauke da juna biyu

10. Ana amfani da garin zogale a cikin abinci domin maganin hawan jini, kuma yana karawa mutum kuzari.

11. Ana amfani da furen zogale, a dafa shi da albasa, yana maganin sanyi.

12. Ana cin danyen ganyen zogale domin maganin tsutsar ciki.

13. Ana amfani da ganyen zogale da 'ya'yan baure a daka su a dinga sha da nono ko kunu yana maganin ciwon hanta.

14. Ga mutum mai fama da kumburi ko sanyin kashi, zai iya amfani da 'ya'yan zogale da man kwakwa a daka a dinga shafawa a wurin da ake jin ciwon.

15. Ana daka zangarniyar zogale tare da 'ya'yan cikinta da kaninfari, masoro, citta da kuma kimba domin karin karfin da namiji da kuma kara masa kuzari, sannan kuma yana karawa mata nishadi.

16. Ana amfani da saiwar zogale da 'ya'yan kankana a daka a dinga sha da nono yana maganin tsakuwar ciki (Apendix).

17. Ana amfani da ruwan daffafen zogale wurin rage radaddin ciwon Aids.

18. Mai fama da cutar malaria, typhoid, ciwon basir, da shawara, zai dinga amfani da ruwan dafaffen zogale domin samun waraka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel