Ikon Allah sai kallo: Wata mata ta haihuwa bayan shafe shekaru 10 dauke da juna biyu

Ikon Allah sai kallo: Wata mata ta haihuwa bayan shafe shekaru 10 dauke da juna biyu

- Wani abun mamaki ya faru da wasu ma'aurata, inda suka kwashe shekaru goma suna jiran haihuwar 'yar su ta biyu

- Matar mai suna Lola ta kwashe shekaru goma ta dauke da juna biyu, wanda alamu suka tabbatar da cewa tana dauke da cikin

- Sai dai kuma sunje asibitoci da dama sun nuna musu cewa babu ciki a tattare da ita, daga karshe dai Allah ya basu haihuwa bayan shekaru goma

Wani abu da ya faru wasu ma'aurata Mista Abiodun Orebela da matarsa Lola, wanda suke zaune a jihar Ogun, hakan ya biyo bayan ma'auratan biyu da suke zaune a unguwar Satellite Town, sun samu haihuwa bayan shafe shekaru 10 suna jiran tsammani.

Ko tantama babu lokacin da suka dauka suna jiran haihuwar zai iya kawo karshen auren da suka yi wanda suka yi na soyayya da ganin mutuncin juna, amma mai makon hakan sai hakan ya karawa soyayyar ta su karfi.

KU KARANTA: Tirkashi: Matata na so na kwanta da kanwarta - Wani magidanci ya koka

Yadda lamarin ya faru

Bayan bikin aurensu a watan July na shekarar 2007, ma'auratan sun samu juna biyu a shekarar da suka yi auren, kuma sun samu haihuwa ta farko. Daga baya Lola ta kara samun juna biyu a karon na biyu, daga nan ne matsalar ta samo asali, saboda jikinta sun nuna cewa tabbas tana da juna biyu.

Amma kuma duk lokacin da suka je gwaji asibitin kudi dana gwamnati sai ya nuna cewa babu juna biyu a tare da ita. Wannan abu ya jawo musu matsala da yawa a cikin dangin mijin dana matar.

Amma cikin shekaru goma suna fama da wannan matsalar, sai Allah ya share musu hawayensu, inda Lola ta samu ta haifi yarinyar da ta shafe shekaru goma tana dauke da juna biyun ta. Sun kuma sanya mata suna 'Miraculous' a turance, ma'ana 'Yar baiwa'.

Wannan lamari dai kusan shine na farko da ya fara faruwa a 'yan shekarun nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel