Tirkashi: Matata na so na kwanta da kanwarta - Wani magidanci ya koka

Tirkashi: Matata na so na kwanta da kanwarta - Wani magidanci ya koka

- Wani mutumi ya koka akan yadda matarsa ke nuna halin ko in kula akan yadda kanwarta ke shigar banza a gidansu

- Ya ce kanwar matar tasa na tada mishi hankali matuka, amma kuma matar tasa ta nuna halin ko in kula

- Mutumin ya bukaci shawara akan yadda zai bullowa lamarin, inda ya bayyana cewa kowanne lokaci ana iya samun matsala

A cewar wani mutumi, ya bayyana cewa akwai yiwuwar matarsa ta na so ya kwanta da kanwarta, ganin yadda kanwarta take yawo cikin kayan bacci a gidansu ba tare da matar tasa tayi mata korafi ba.

Ga abinda mutumin ya rubuta a shafinsa:

"Ina mutukar bukatar taimako akan yadda zan bullowa wannan matsalar. Kanwar matata tazo gidanmu sati uku da suka wuce domin ta zauna damu. Shekarunta 22. Matsala ta daya da ita shine yadda take yin shiga a cikin gidanmu, kuma matata taki lura da hakan.

"Kullum ba ta da kayan sawa idan ba masu nuna surar jikinta ba, da kuma kayan bacci. Tana da jiki da diri mai kyau kuma koda yaushe tana son ta dinga nuna jikinta. Ban san yadda zan sanar da matata ba akan ta yiwa kanwarta magana ta dinga sanya kayan da zasu dinga rufe jikinta. Za ta iya jin haushi taga kamar kanwarta na jan hankali na.

KU KARANTA: Akwai sauran rina a kaba: Dalilai 19 da zasu iya sawa Abba Gida-Gida yayi nasara akan Ganduje a kotu - Ashafa Murnai

"Lokacin hutun sallah, ni da ita ne kawai a gida, saboda matata bata yin sallah a garin da muke. Hakan yasa dole na bar mata gidan na koma Otal da zama.

"Yau da safe na dakko kayan bacci na zan wanke, sai take cewa na bata zata wanke, kuma lokacin zani ne kawai a jikinta, saboda za ta je wanka ne lokacin, komai na jikinta ya fito kuma ba ta damu ba.

"Shekarar mu daya da yin aure, kuma ban taba cin amanar matata ba, kuma ita ma ta yadda dani, amma gaskiya kanwarta na tada mini hankali matuka.

"Dan Allah ina neman shawara akan yadda zan bullowa wannan lamarin."

Akan samu matsaloli irin wannan a gidajen masu aure musamman wadanda suka aminta da kannansu su zauna a gidajen su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng