Dabi'u 7 da ke raunata garkuwar jikin mutum

Dabi'u 7 da ke raunata garkuwar jikin mutum

Akwai wasu sinadarai da halittu a cikin jinin mutane da ke basu kariya daga kwayoyin cuta da kan iyya kassara lafiyar jikin mutum.

Kwayoyin cuta zasu samu hanyar shiga da kama wurin zama a jikin mutum idan garkuwar jikinsa ta samu rauni.

Kwararru a bangaren harkar lafiya sun gano wasu dabi'u har guda 7 da ke raunata garkuwar jikin mutum:

1. Cin tarkacen abinci: Koshin lafiya ya dogara kacokan da irin abincin da mutum ya ke ci. Yawan cin abinci masu sukari da maiko na raunana garkuwar jiki. Jiki na bukatar sinadaran 'vitamins' da karin wasu sinadaran masu yawa da zasu karfafa garkuwar jikinsa.

Masana sun bayar da shawarar yawan cin ganye a kowanne abinci ko da kuwa babu yawa.

2. Rashin samun hutu: Yawan aiki ba tare da samun isashshen bacci ba yana matukar taba aikin sinadaran jikin da ke kai sako kowanne bangare (Hormones). Matukar sinadaran kai sako sun samu matsala, jiki ba zai ke samun sako ba idan kwayoyin cuta sun shiga. Daga nan sai mutum kullun ya yi ta fama da rashin lafiya.

3. Rashin motsa jiki: Zama wuri guda ba tare da motsa jiki ba yana raunana garkuwar jiki. Yawan cin abinci da rashin motsa jiki na saka muguwar kiba wacce ke hana garkuwar jiki yin aiki cikin sauki.

Yana da kyau mutum ya ware lokacin motsa jiki ko da sau daya ne a cikin kowanne sati ko wata.

DUBA WANNAN: Yadda Tinubu da shugabannin kabilar Yoruba suka ci amanar Abiola a 1993 - Sule Lamido

4. Rashin samun isashshen bacci: Kammar yadda gajiya ke illata jiki, haka ma bacci ke yi wa jiki. Bacci na taimaka jiki da kwakwalwa su samu wartsake wa. Rashin samun isashshen bacci na gajiyar da jiki tare da saka garkuwar jiki yin sanyi.

5. Zukar hayaki: Zukar hayaki na taba dukkan sassan jikin mutum, musamman hanta da koda. Bayan hakan, sinadarin da ke cikin sigari (Nicotine) na rage karfin garkuwar jikin mutum.

6. Matsananciyar kishin ruwa: Shan isashshen ruwa mai tsafta na taimaka wa wajen wanke sinadarai masu illa daga cikin jini. Kusan kaso 60% na jikin mutum na dauke da ruwa ne. Jiki ya dogara da ruwa domin gudanar da muhimman aiyuka a jikin mutum.

7. Kazanta: Hatta karamar kazanta, kamar rashin wanke hannu kafin cin abinci ko kuma rashin wanke baki kafin a kwanta, kan iya raunata garkuwar jiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel