'Yunwa zata kashe mu'- Inji wasu mazauna a Sokoto
-Harin da aka kai a kauyen Rakwabni na Jihar Sokoto a ranar a sabar ta satin da ya gabata ya bar baya da kura, inda al'ummar garin suka koka dalilin rashin yin nomada
-Mai garin Kurya yace ya sauke yan gudun hijira fiye da mutum 4,000
-Shugaba hukumar zakka da wakafi ta jihar, Malam lawal Maidoki, ya ce gwamnati ta tura da motoci 10 na kayan abinci don a rabba ma mutanen kauyen da abun ya shafa
Harin da aka kai ranar Asabar din da ta gabata wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutum 25 a wasu kauyuka na karamar hukumar Rabah dake jihar Sokoto ya bar baya da kura.
Kauyen Rakwabni ne aka fi yima barna inda aka kashe mutum sha bakwai ciki hadda yarinya yar shekara 6. Garin na kilomita 7 ne daga garin Gandi dake a Rabah, inda a halin yanzu mazauna garin duk sunyi kaura.
Bayan sun gama hargitsa garin, yan ta'addan sunyi awon gaba da shanun al'ummar garin wanda suke amfani dasu wajen aikin gona.
Wasu Kauyukan da abin ya shafa sun hada da Bedi, Kalfu-Tsege, Kwalfa Agaji, da Kaiwa gari.
Babban limamin garin Rakwabni kuma shugan yan banga na kauyen, Malam Dahiru, ya ce kafin akai harin, Rakwabni ne kadai kauyen da ya rage ba akai ma hari ba.
Ya ce "Mu a Rakwabni muna da kwarewa sa'annan muna shiga aikin tsaro na sa kai, saboda haka muna ba yan ta'adda matsala."
Malam Dahiru ya kara da cewa sau dayawa suna fuskantar yan ta'adda su kwace shanun da suka sato daga mutane sa'annan su mayar ma mutane da shanunsu.
Yace "Sabida haka wannan harin da suka kawo ramuwar gayya ce saboda abinda muke masu"
Ya kara da cewa "Yan ta'addan sun san basu iya mana, shi yasanya sukayi mana kwantan bauna. Mun samu labari sun zo saman mashina fiye da 50 da kuma mota Hilux"
Ya bayyana cewa babu mutum guda cikin yan kungiyar tsaro ta sa kai da aka kashe. Wadanda aka kashe mutanen da basu da makamai ne marassa karfi.
Haka zalika mai garin Rakwabni, Yusuf Idris, a lokacin da yake zantawa da jaridar Daily Trust, ya bayyana yadda ya sha da kyar a lokacin da aka kawo harin
Ya bayyana cewa a lokacin yana masallaci "Sai naji harbin bindiga, kafin kace me sai na sake jin ana ta harbin, kafin na ankara sai na ga yan ta'addan akan babura sun zagaye wajen da nike."
ya kara da cewa "Na godema Allah mashin dina na kusa kuma yana da lafiya sosai, dan danan sai na tada shi na tsere, sunyi kokarin su kamo ni amma nayi dubara na tsere inda daga nan na kira waya don a kawo mana dauki."
KARANTA WANNAN: Buhari ya umurci CBN da su sa ido akan masu shigowa da Manja
Mazauna kauyen sun bayyana damuwarsu game da harin, saboda an dagula masu aikin noma daidai lokacin da za a fara shuka. Sunyi kira ga gwamnati da ta sanya matakan tsaro.
Wani daga cikin mazauna kauyen yace "Idan bamuyi noma ba wannan shekarar to da me za mu ciyar da iyalanmu? yunwa zata kashe mu ne."
Mai garin kauyen Kurya, Dangaladima Muhammadu Bello, ya ce a yanzu haka a kwai yan gudun hijira fiye da mutum 4,000 da ya sauke a garin. Ya roki gwamnatin jihar da ta sanya matakan tsaro a Rakwabni don mutanen garin su samu su koma.
Gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal ya basu tabbaci cewa suna kokari tare da gwamnatin tarayya don ganin an magance matsalolin tsaro dake addabar garin.
Shugaban hukumar zakka da wakafi ta jihar Alhaji Lawal Maidoki, ya ce gwamnatin jihar ta kai manyan motoci 10 na kayen masarufi don a rabba ma al'ummar da abin ya shafa.
Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng