An nada sabon kwamishinan 'Yan sanda a Zamfara

An nada sabon kwamishinan 'Yan sanda a Zamfara

Usman Nagogo ya kama aiki a matsayin sabon kwamishinan 'Yan sanda na jihar Zamfara bayan an yi wa tsohon kwamishinan, Celestine Okoye canjin wurin aiki zuwa hedkwatan hukumar da ke Abuja.

Sanarwar ta fito ne daga bakin mai magana da yawun rundunar, SP Muhammad Shehu cikin wata jawabi da ya fitar a ranar Juma'a.

Ya ce kafin a kawo shi Zamfara, shi ne ke kula da sashin sa ido kan ayyuka a hedkwatan rundunar da ke Abuja.

Ya ce Nagogo ya shiga aikin dan sanda ne a 1990 a matsayin mataimakin sufritanda na 'yan sanda.

DUBA WANNAN: Hanyoyi 5 da ake gane takardan naira ta jabu

Ya kara da cewa bayan samun horo a kwallejin 'yan sanda, Nagogo ya yi aiki da rundunar 'yan sanda reshen jihar Kwara na tsawon shekara guda kuma daga bisani ya yi ayyuka a wurare daban-daban.

A cewarsa, Nagogo ya yi aiki a sashin binciken kisan gilla, sashin yaki da masu fashi da satar mota, sashin kudi da kuma DPO a rundunar 'yan sanda da ke Rogo duk a jihar Sokoto.

Shehu ya ce an haifi Nagogo a garin Sifawa a karamar hukumar Bodinga na jihar Sokoto kuma ya yi karatu a Ahmadu Bello Academy da ke Farfaru a Sokoto inda ya kammala a 1982.

Ya kuma yi karatun digiri a Jami'ar Usmanu Danfodio da ke Sokoto a 1987 sannan ya yi karatun digiri a fanin lauya a 1998 kuma ya tafi makarantar koyan aikin lauya da ke Buari Abuja a 2004.

Shehu ya ruwaito cewa Nagogo ya tabbatar wa mutanen Zamfara cewa za a inganta tsaro a jihar bisa tsarin dokar aiki.

Nagogo ya yi kira ga mutanen jihar su bawa rundunar goyon baya ta hanyar taimaka ma ta da bayannai masu amfani kuma kan lokaci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel