Hukumar Kwastan na tara N5.5bn a kowace rana – Hameed Ali

Hukumar Kwastan na tara N5.5bn a kowace rana – Hameed Ali

- Hukumar kwastan tace tana tattara akalla naira biliyan 5.5 a kowace rana

- Shugaban hukumar, Hameed Ali ne ya bayyan hakan a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni

- Ali yace an samu wannan karin kudaden shiga ne dalilin mayar da tsarin tattara kudaden shiga da aka yi zuwa na zamani a kowace tashar jiragen ruwan kasar

Shugaban hukumar kwastan na Najeriya, Hameed Ali, ya bayayyana cewa hukumar na tara akalla naira biliyan 5.5 a kowace rana.

Ali ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni yayinda ya ziyarci hedikwatar kungiyar dillalan fiton kayan da ake shigowa da su ta ruwa (NAGAFF), a ofishin su da ke jihar Lagas.

Shugaban na Kwastan ya kara da cewa an samu wannan karin kudaden shiga ne dalilin mayar da tsarin tattara kudaden shiga da aka yi zuwa na zamani a kowace tashar jiragen ruwan kasar.

Ya kara da cewa wannan karin samun kudaden shiga ya sa hukumar kwastan na biyan albashi ma’aikatan ta a kan lokaci, kuma tsarin ya kara maida hukumar daya daga cikin muhimman hukumomin da gwamnatin tarayya ke takama da ita wajen samar da kudaden shiga.

“Wannan tsari ya haifar da hanyoyin shigar kudade aljihun gwamnati kai tsaye kuma a cikin sauki a tashoshin jiragen ruwa da kuma kan iyakokin kasar nan.

KU KARANTA KUMA: Sadiq Kurba ya zama kakakin majalisar Gombe

“Ya kuma magance duk wata hanyar da kudade za su rika sulalewa, kasancewa kai tsaye ake biyar kudade, ba tare da an yi cudanya tsakanin mai biyan kudi da mai karbar wa gwamnatin kudaden ba."

Ya kuma ja kunnen ‘yan kungiyar da su rika gudanar da ayyukan su a bisa ka’dojin da gwamnati ta gindiya, ba tare da kumbiya-kumbiya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel