Shugaban majalisar dinkin duniya ya jinjinawa shugaba Buhari a kokarin da yake na yaki da cin hanci

Shugaban majalisar dinkin duniya ya jinjinawa shugaba Buhari a kokarin da yake na yaki da cin hanci

- Babban sakataren majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres, ya jinjina wa shugaba Buhari kan mutuncinsa da kumayaki da rashawa

- Mohammad Ibn Chambas, wakilin majalisar dinkin duniya na musamman a Afrika ta yamma ne ya isar da sakon Guterres zuwa ga Buhari

- Shugaba Buhari yace ya ji dadin yadda majalisar UN ta nuna farin ciki da yaki da rashawar da gwamnatinsa ke yi, yaki da talauci da kuma kokarin tabbatar da daidaituwar lamura a yankin

Babban Sakataren majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres yajinjina wa karamcin shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Mohammad Ibn Chambas, wakilin majalisar dinkin duniya na musamman a Afrika ta yamma ne ya isar da sakon Guterres zuwa ga Buhari a jiya Alhamis, 13 ga watan Yuni a fadar shugaban kasa, Abuja.

Ya yabi “kirki da mutuncin Buhari a matsayin mai kishin kasa, musamman wajen yaki da rashawa tare da tabbatar da gaskiya a cikin al’umma.”

Ya bayyana cewa majalisar ta yaba da jajircewar shuwagabannin Najeriya wajen magance talauci, ta’addanci, da kuma inganta tafkin Chadi.

Chambas yayi alkawarin cewa majalisar za ta ci gaba da ba hukumar zabe mai zaman kanta goyon baya ta fannin fasaha a zabbukan da za a gudanar nan gaba.

KU KARANTA KUMA: Umarninka kawai muke jira - Majalisar dokokin tarayya ta sanar da Shugaba Buhari

Har ila yau ya bayyana farin cikin majalisar cewa an zabi wakilin Najeriya na dindindin, Farfesa Tijjani Muhammad Bande a matsayin shugaban taron majalisar a karo na 74.

Shugaba Buhari yace ya ji dadin yadda majalisar UN ta nuna farin ciki da yaki da rashawar da gwamnatinsa ke yi, yaki da talauci da kuma kokarin tabbatar da daidaituwar lamura a yankin

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel