Idris Kareka ya dare kujerar Kakakin Majalisar Dokoki ta jihar Jigawa.

Idris Kareka ya dare kujerar Kakakin Majalisar Dokoki ta jihar Jigawa.

- Idris Kareka ya sake zamowa kakakin majalisar dokoki ta jihar Jigawa karo na biyu

- An zabi Kareka a matsayin kakakin Majalisar Jigawa ba tare da abokin hamayya ba

Hon. Idris garba kareka ya samu nasarar darewa kujerar kakakin majalisar dokoki ta jihar Kaduna a yau ranar Alhamis.

Kareka wanda dama shine tsohon kakakin majalisar da ta gabata, kuma shike wakiltar al'ummar Jahun.

Kakakin majalisar, an sake zabarsa a matsayin kakakin majalisar jahar ta bakwai, kuma tuni ya karbi rantsuwa.

Haka zalika, an zabi Hon.Liman Musa Kusada, dan majalisa mai wakiltar al’ummar Guri a matsayin Mataimakin Kakakin majalisar.

Yan jarida sun ruwaito cewa kareka da mataimakinsa an zabe su ne ba tare da abokan hamayya ba.

KARANTA WANNAN:Aisha Buhari ta je taro sanye da rigar miliyan 1.6

A jawabinsa, Kareka ya tabbatarwa mutanen jihar cewa zasu hada karfi da karfe da Majalisar zartaswa ta jihar suyi aiki tukuru don cigaban jihar.

“A shirye muke da mu hada kai da sauran bangarori na gwamnati don cigaban jiharmu”

Gwamnan jihar Muhammad Badaru da mataimakinshi Umar Namadi sun halarci kaddamarwar majalisar.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zaumunta

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar

jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel