Bagudu ya ki tabbatar dani a matsayin Alkalin Alkalai saboda ni kirista ce, inji Alkalin Alkalai
Mukaddashiyar Alkalin Alkalan jahar Kebbi, Esther Asabe Karatu ta kai karar gwamnan jahar Kebbi, Atiku Bagudu gaban majalisar sharia ta kasa inda take zarginsa da nuna mata wariya da bambamcin addini wajen tabbatar da ita a matsayin Alkalin Alkalan jahar.
Cikin korafin da Esther ta aika ma majalisar wanda jaridar Daily Nigerian ta yi ido dashi, ta zargi gwamnan da kin tabbatar da ita wannan babban mukami kawai don ita Kirista ce ba Musulma ba.
KU KARANTA: Da arziki a gidan wasu: Mata 2000 daga jahar Adamawa sun ci albarkacin Aisha Buhari
Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar 17 ga watan Janairun 2019 ne majalisar dokokin jahar Kebbi ta tantance Esther tare da amincewa da ita a matsayin Alkalin Alkalan jahar, amma gwamnan ya ki tabbatar da ita akan wannan mukami.
Haka zalika gwamnan ya hana ma Esther daman ta rantsar dashi a yayin daya karbi rantsuwa a matsayin gwamnan jahar Kebbi karo na biyu, inda yasa babban Alkalin kotunan shari’ar Musuluncin jahar, Mukhtar Imam Jega ya rantsar dashi.
Bugu da kari Alkali Esther na gab na yin ritaya daga aiki, sakamakon zata cika sharuddan yin ritaya daga Alkalanci a ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2019, wanda hakan ke alanta da gangan gwamnan ke jan kafa kan bukatar Esther har sai ta yi murabus.
Sai dai sakataren gwamnatin jahar Kebbi, Babale Yauri ya musanta zargin Esther, inda yace babu yadda za’ayi gwamnan ya tabbatar da ita a matsayin Alkalin Alkalai bayan majalisa bata tantanceta ba, yace majalisar hakan ya faru ne saboda akwai rudani a cikin takardun karatunta.
Don haka yace wasikar da aka ce majalisar ta aika ma gwamna inda take shawartarsa ya tabbatar da Esther a matsayin Alkalin Alkalai ba gaskiya bane, wasikar bogi ce saboda babu sa hannun kowa akanta.
Daga karshe Alkali Esther tayi gargadi kada gwamnan ya nada mai sharia Mohammed Sulaiman Ambursa a matsayin Alkalin Alkalai saboda a cewarta mutum ne mai bakin cin rashawa kuma aboki ne ga yan siyasa.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng