Labari cikin hotuna: Shugaba Buhari da Shugabannin kasashe jiya a Abuja

Labari cikin hotuna: Shugaba Buhari da Shugabannin kasashe jiya a Abuja

A jiya Laraba, 12 ga Watan Yuni, 2019, ne aka yi bikin murnar Ranar Damukaradiyya a Najeriya, inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ci, ya sha tare da sauran shugabannin kasashen Afrika.

Labari cikin hotuna: Shugaba Buhari da Shugabannin kasashe jiya a Abuja

Shugaba Buhari da Mataimakin sa su na gaisawa da Shugabannin kasashe
Source: Twitter

Shugaban kasar ya gayyaci sauran Takwarorinsa na Afrika wajen bikin tunawa da wannan babbar rana a kasar. An yi wannan taro ne a Abuja, wanda daga baya kuma aka shirya walima cikin dare.

Labari cikin hotuna: Shugaba Buhari da Shugabannin kasashe jiya a Abuja

Shugaba Buhari ya na jawabi a gaban Shugabannin Duniya
Source: Instagram

Daga cikin wadanda su ka halarci wannan babbar liyafa da aka shirya akwai; shugaba Hage Geingob na kasar Namibia; shugaban kasar Liberia George Weah; da Macky Sall na kasar Sanagal.

Labari cikin hotuna: Shugaba Buhari da Shugabannin kasashe jiya a Abuja

Shugaba Buhari da Mai dakin sa Hajiya Aisha Buhari
Source: Twitter

Haka zalika, Patrice Talon na kasar Benin mai makwabtaka da kasar ya halarci wannan liyafa da aka yi a fadar shugaban kasa. Shi ma Paul Kagame wanda ya na Najeriya, ba a bar sa a baya ba.

KU KARANTA: Yaudarar Duniya ake yi da da yaki da Barayi a Najeriya - Frank

Labari cikin hotuna: Shugaba Buhari da Shugabannin kasashe jiya a Abuja

Shugaba Buhari a tsakiyar Mai dakin sa da wani Shugaban kasa
Source: Instagram

Haka mataimakin shugaban kasar Najeriya watau Farfesa Yemi Osinbajo ya halarci wannan biki da aka yi. An kuma hangi manyan Jakadun kasashen ketare da ke Najeriya a fadar shugaban kasar.

Labari cikin hotuna: Shugaba Buhari da Shugabannin kasashe jiya a Abuja

Manyan Shugabannin Kasashen Afrika a cikin fadar Aso Villa
Source: Instagram

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel