Da arziki a gidan wasu: Mata 2000 daga jahar Adamawa sun ci albarkacin Aisha Buhari

Da arziki a gidan wasu: Mata 2000 daga jahar Adamawa sun ci albarkacin Aisha Buhari

Uwargidar shugaban kasar Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari ta bada tallafi ga mata dubu biya a garin Yola, babban birnin jahar Adamawa a wani taro daya gudana a babban dakin taro na fadar gwamnatin jahar.

Legit.ng ta ruwaito an gudanar da wannan aikin bada tallafi ne a ranar Talata, 12 ga watan Yuni, kuma gidauniyar Aisha Buhari ce ta dauki wannan taro tare da hadin gwiwar hukumar NDE inda mata dubu biyu daga sassa daban daban na jahar Adamawa suka dace da samun tallafin.

KU KARANTA: Za mu cigaba kamar yadda China da India suka cigaba – Shugaba Buhari

Da arziki a gidan wasu: Mata 2000 daga jahar Adamawa sun ci albarkacin Aisha Buhari
Da arziki a gidan wasu: Mata 2000 daga jahar Adamawa sun ci albarkacin Aisha Buhari
Asali: Facebook

A yayin taron, Aisha ta raba ma mata dubu daya masu kananan sana’o’i kamar masu kosai, waina, zobo da ire irensu tallafin naira dubu goma goma, yayin da za’a horas da wasu rukunin mata 550 akan sana’o’in hannu daban daban.

Shugaban hukumar NDE ta kasa, Dakta Nasir Ladan ya bayyana cewa akwai wasu mata guda 50 da za’a basu horo akan sana’ar gyaran wayoyin hannu, sai kuma wasu mata guda 400 da zasu samu horon akan dabarun kwalliya.

A cewar Ladan, Aisha ta kirkiri wannan aiki ne da nufin taimaka ma mata da matasa sakamakon an yi biri dasu a baya, don haka a yanzu take muradin shigo dasu sahun gaba domin a dama dasu.

Ita ma a nata jawabin, uwargidar shugaban kasa ta tabbatar da cewa mata da dama basu bukatar wani babban jari kafin su dogara da kansu, inda tace da da kudi kalilan zasu iya fara sana’ar da zasu kula da kansu da iyalansu.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai matan shuwagabannin kasashen Nijar, Ghana, Chadi, Gambia da kuma Kwadebuwa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel