Zan kashe N208bn wajen inganta gine-ginen jami'o'i a Najeriya - Buhari

Zan kashe N208bn wajen inganta gine-ginen jami'o'i a Najeriya - Buhari

Babban bako yayin bikin yaye dalibai karo na 23 da aka gudanar a jami'ar Abuja, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba jajicewar wajen magance kalubalai da jami'o'in kasar nan ke fuskanta.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, shugaban kasa Buhari ya ce gwamnatin sa ta daura damarar share hawayen jami'o'in kasar nan musamman wajen inganta gine-ginen us da kuma harkokin gudanarwa.

Shugaba Buhari wanda ya kasance babban bako yayin bikin yaye dalibai karo na 23 da aka gudanar a jami'ar Abuja, ya ce a halin yanzu gwamnatin sa ta bayar da lamunin kashe kimanin Naira biliyan 208 domin habaka ci gaban jami'o'i a kasar nan.

Buhari wanda babban sakataren ma'aikatar ilimi Arc. Sonny Echono ya wakilta yayin bikin a garin Abuja, ya ce gwamnatin sa ta shimfida tsare-tsare a habakar ci gaban gine-ginen jami'o'i domin magance nakasun da harkokin ilimi na kasar nan ke fuskanta a yanzu.

KARANTA KUMA: Najeriya ta samu ribar N85trn ta kudin man fetur cikin shekaru biyar

Buhari ya kum yabawa shugaban jami'ar Abuja, Farfesa Michael Adikwu, da kuma sauran jagorori masu rike da madafan iko na gudanarwar ta musamman dangane da yadda al'amura ke gudana cikin daidaito na zaman lafiya da hadin kai a jami'ar.

Yayin taya murna ga dalibai kimanin 5,288 da jami'ar ta yaye a bana, shugaban kasa Buhari ya nemi da su ribaci ilimin su wajen bayar da mafificiyar gudunmuwa ta bunkasa tattalin arziki a kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel