Tirkashi: Barayi sun sace cinikin Sallar da aka yi a gidan Zoo na Kano

Tirkashi: Barayi sun sace cinikin Sallar da aka yi a gidan Zoo na Kano

- An wayi gari an tarar barayi sun yiwa baitul malin gidan Zoo na jihar Kano tatas

- Rahotanni sun nuna cewa kudin da barayin suka sace wanda aka yi ciniki ne a lokacin bukukuwan karamar sallar nan da ta gabata

- Sai dai kuma hukumar 'yan sandan jihar ta Kano ta bada sanarwar cewa ta kama wasu wadanda take tunanin suna da hannu a lamarin

Wani abu da ya faru mai kama da almara a jihar Kano, yayin da aka sace duka cinikin da aka yi na wadanda suka shiga gidan Zoo na Kano a wannan karamar sallar.

Da farko dai gidan rediyon Freedom da ke Kano shine ya fara ruwaito labarin cewa bayan an yi cinikin kwanakin bukukuwan sallah, kawai sai aka wayi gari an nemi kudin sama da kasa an rasa.

KU KARANTA: Jerin 'yan wasa guda 10 da suka fi kowa daukar albashi mai yawa a duniya

Ma'aikatan gidan Zoo din sun bayyana cewa wadansu mutane ne wadanda ba a san ko su waye ba suka shiga inda ake ajiye cinikin, suka kwashe komai, ko anini basu bari ba.

Sai dai kuma wasu rahotanni da aka samu a gidan Zoo din, sun bayyana cewa an kama wasu daga cikin ma'aikatan gidan Zoo din, inda ake zargin su da hannu a cikin lamarin.

A nasu bangaren rundunar 'yan sandan jihar Kano, ta bakin mai magana da yawun rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa sun kama mutanen da ake zargin suna da hannu a wannan ta'asa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel