Sani Haruna: Ban san yawan mutanen dana kashe ba a shekara daya

Sani Haruna: Ban san yawan mutanen dana kashe ba a shekara daya

- Sani Haruna ya ce baai san yawan mutanen da ya kashe ba a shekara daya

- Yace shine yake kula da mutanen da aka yi garkuwa dasu, sannan kuma shine wanda yake harbe dukkanin wadanda suka kasa biyan kudin fansa

- Ya ce yana rokon gwamnati ta bashi dama domin ya taimakawa hukumomin tsaro wajen kama 'yan ta'adda

Gawurtaccen mai garkuwa da mutanen nan, Sani Haruna wanda aka fi sani da Gayu, wanda rundunar 'yan sandan shugaban hukumar 'yan sanda na kasa ta kama ya bayyanawa jaridar Vanguard cewa ya ba zai iya rike yawan mutanen da ya kashe ba saboda sun ki biyan kudin fansa.

A wata hira da aka yi dashi a Abuja, mutumin dan shekara 20 a duniya, ya ce shi baya fita kamo mutane, sai dai a kamo a kawo mishi.

Ya ce shine aka bai wa damar kashe duk wani mutumi da ya kasa biyan kudin fansa, wanda shugaban su yake tambayarsu.

Ya ce tunda shine yake da alhakin kashe mutanen da suka kasa biyan kudin fansa, shugabansu yayi masa koyarwa ta musamman, wurin yadda ake rike bindiga musamman AK47, wacce ya bayyana a matsayin bindigar da masu garkuwa da mutane suka fi so.

Sani Haruna, wanda yayi hira da jaridar Vanguard cikin harshen Hausa, ya roki gwamnatin tarayya ta bashi damar shiga cikin sojoji domin taya su bayyana sauran 'yan uwansa da suke aiki tare a jihohin Katsina, Zamfara da kuma kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

KU KARANTA: Hotuna: Wani babban Limami ya mutu a daidai lokacin da yake hudubar Juma'a a masallaci

"Sunana Sani Haruna, ni ne nake kula da wadanda aka kamo a wurin da muke tsare su a cikin dajin Katsina. Yanzu shekara ta daya kenan ina wannan aikin. Kafin na fara wannan aikin, da ni makiyayi ne. Daga kiwon shanu shine na komo yin wannan harka ta garkuwa da mutane, wanda shugaban su ya gayyace ni."

Ya ce ya shiga harkar garkuwa da mutane ne bayan ya samu shugabansu ya tambaye shi cewa yana son aikin yi, bayan barayin shanu sun sace mishi shanunsa.

Da aka tambayeshi yawan mutanen da ya kashe a shekarar da ya shafe yana aikin, Haruna ya bayyana cewa: "Tsakani da Allah, ban zan iya kirga yawan mutanen dana kashe ba, saboda bana kirgawa, amma dai na san na kashe mutane da yawan gaske."

Da aka tambayeshi mai yaso gwamnati tayi masa yanzu, ya ce idan ya samu aka sake shi, zai hada kai da hukumomin tsaro domin taimaka musu gurin zakulo 'yan ta'addar, tunda ya riga yasan dukkanin shige da ficensu, ya kuma san guraren zaman su.

Idan ba a manta ba mun kawo muku rahoton cewa ranar 3 ga watan Yuni, 2019, an gabatar da Haruna bayan jami'an 'yan sanda sun cafke shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel