Abubawa 5 da ya kamata ku sani kan sabon kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila

Abubawa 5 da ya kamata ku sani kan sabon kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila

A yau Talata 11 ga watan Yuni ne Honarabul Femi Gbajabiamila ya yi nasara zama Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya ta 9 bayan ya doke Umar Bago da kuri'u 205 a zaben da aka gudanar.

Ga wasu muhimman abubuwa biyar da ya dace ku sani game da sabon kakakin majalisar.

1 - An zabi shi zuwa Majalisar Wakilai ne tun 2003 domin wakiltan Surulere shiyya ta I na Jihar Legas. Ya rike mukamamin shugaban marasa rinjaye a Majalisa ta shida da bakwai. Har ila yau, shine shugaban marasa rinjaye na Majalisa ta takwas.

DUBA WANNAN: Takarar shugabancin majalisa: Dalilai 5 da suka sa Lawan ya kayar da Ndume

2 - Ya yi karatu a Najeriya, Amurka da Ingila. Ya yi karatu a Kwallejin Igbobi da ke Yaba a Legas sannan ya tafi King William's College da ke kasar Ingila. Ya kuma yi karatu a John Marshall Law School da ke Chicago a Illinois da kuma Jami'ar Legas (UNILAG) inda ya samu digiri a fannin aikin Lauya.

3 - Gbajabiamila ya takawa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo birki yayin da ya ke neman zarcewa kan mulki karo na uku inda ya yi tilasta aka yi amfani da wani sashi na doka da ta bawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya zama shiugaban kasa na riko a 2009.

Gbajabiamila ne dan majalisa na farko da ya ki karbar lambar karramawa ta kasa.

4 - Ya yi aiki a matsayin lauya a jihar Georgia a kasar Amurka kafin ya dawo Najeriya a 2002.

5 - Daya daga cikin dokokin da Gbajabiamila ya gabatar da majalisa sun hada dokar yi wa Hukumar Sadarwa ta Najeriya, 2013 garambawul wadda ta bawa hukumomin tsaro amfani da hanyoyin sadarwa don gano 'yan ta'adda; Dokar Babban Bankin Najeriya ta 2012 don inganta tsare-tsaren kudi a kasa; Dokar kare gine-ginen gwamnati na 2011 don kulawa da gine-ginen gwamnati da sauran su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel