Al'ummar Yobe sun tsuduma cikin farin ciki kan nasarar Ahmed Lawan

Al'ummar Yobe sun tsuduma cikin farin ciki kan nasarar Ahmed Lawan

Al'ummar Yobe, jihar sabon Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan sun bayyana farin cikin su kan nasarar da ya samu na zama jagora a majalisar inda suka ce hakan alama ce da ke nuna kishin kasa.

Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyin su yayin da ake rantsar da sabon shugaban majalisar a Abuja yayin hira da su kayi da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) a garin Damaturu a ranar Talata.

Sanata Ahmad Lawan na jam'iyyar APC daga jihar Yobe ne ya yi nasarar zama shugaban majalisar bayan ya doke Sanata Ali Ndume a zaben da a kayi ranar Talata.

Lawan ya samu kuri'u 79, yayin da Ndume ya samu kuri'u 28.

Alhaji Muhammad Gagiyo (Zanna Dujima na Bade) ya ce zaben Lawan zai kawo cigban kasa.

DUBA WANNAN: Har yanzu Ganduje da Sanusi ba su yi sulhu ba - Hadimin Gwamna

Ya ce: "Yanzu Najeriya ta samu shugaban majalisa mai kaunar yi wa kasa hidima tare da inganta rayuwar al'umma.

"Tsawon shekaru da suka gabata, sabon shugaban majalisar ya bayyana gwazo da wakilci na gari a mazabar sa. Muna fatan zai yi jagoranci na gari a majalisar domin kawo cigaba a kasar."

Muhammad Gagiyo ya bukaci sauran 'yan majalisar su bawa sabbin shugabanin hadin kai domin inganta rayuwar 'yan Najeriya.

Alhaji Ibrahim Usman, wani dan jam'iyyar APC a Yobe, ya ce sabbin shugabanin majalisar za su bayar da gudunmawa wurin ciyar da Najeriya gaba.

Ya kara da cewa, "Sanata Ahmed Lawan yana da kwarewar da zai samar da ingantaccen shugabanci a majalisar."

Wani jagoran al'umma, Alhaji Mamman Suleiman (Majidadin Bade) ya ce zaben Lawan ya zo a dai-dai lokacin da ake bukatar wanda zai tallafawa Shugaba Muhammadu Buhari kaddamar da shirye-shiryen sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel