Dan APC wanda PDP ta mara wa baya ya zama kakakin majalisar Sokoto

Dan APC wanda PDP ta mara wa baya ya zama kakakin majalisar Sokoto

Bayan ya samu mafi yawan kuri’u, Hon. Amin Achida (APC/Wurno) ya zama sabon kakakin majalisar dokokin jihar Sokoto a ranar Talata, 11 ga waan Yuni, a taron rantsar da majalisar dokokin na tara.

Achida ya kayar da dan takarar da jam’iyyarsa ta APC ta tursasa wato Abdullahi Garba Sidi, mai wakiltan yankin Gwadabawa ta kudu.

Zababbu mambobin majalisa 30 karkashin jagorancin mukaddashin magatakardar majalisar dokokin jihar, Alhaji Abdulrazak Shehu ne suka gudanar da zaben.

Ibrahim Sarki (PDP- Sokoto North II) ne ya gabatar da Achida wanda ya samu kuri’u mafi rinaye wajen zama kakakin majalisar.

Achida ya yaba ma mambobin majalisar da suka bashi damar da zai jagorance su, sannan ya basu tabbacin shugabanci mai inganci don ci gaban jihar.

Ya taya dukkanin mambobin majalisar murnar kasacewa daga cikin yan majalisar sannan ya nemi hadin ansu don samun nasara a ayyukan da ke gabansu.

KU KARANTA KUMA: Kai tsaye: Yadda zaben mataimakin shugaban majalisar dattawa ke gudana

A wani labarin kuma Legit.ng ta rahoto a baya cewa Yakubu Saliu Danladi, matashi mai shekaru 34, ya zama shugaban majalisar dokokin jihar Kwara.

Wannan shine karo na farko da Danladi ya fara zuwa majalisar dokokin bayan ya lashe zabe a karkashin inuwar jam'iyyar APC daga mazabar Ilesha-Gwanara.

Honarabul Saheed Popoola, mamba a majlisar daga mazabar Balogun-Ojomu da ke karamar hukumar Offa, ne ya fara bayyana sunan Danladi a matsayin wanda zai jagoranci majalisar kafin daga bisani ya samu goyon bayan abokinsa honarabul Haliru Danbaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng