Hankula sun tashi yayin da abokan ango 6 suka mutu a gidan biki
Hankula sun tashi matuka, hawaye sun kwarara yayin da wasu mutane su 6 suka sheka barzahu a garin Mbieri, cikin karamar hukumar Mbaitoli na jahar Imo, a lokacin da suka halarci bikin auren dan uwansu, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.
Majiyar Legit.ng ya ruwaito kaakakin rundunar Yansandan jahar, Orlando Ikeokwo ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Litinin, 10 ga watan Yuni, inda yace lamarin ya faru ne a daren Lahadi a gidan kanin uban amarya, Herbet Uzoukwu.
KU KARANTA: Yan bindiga sun kai hari jami’ar Filato, sun bindige dalibi har lahira
Kaakakin yace Mista Herbert da kansa ya kai rahoto ga Yansanda, inda yace abokan angon sun rakashi zuwa gidan dangin amaryar da zai aura ne don gudanar da bikin daurin aure na gargajiya, amma sai suka kwana a gidansa sakamakon dare yayi.
Amma ganin gari waye a ranar Litinin, amma mutanen basu farka bane yasa hankalin Herbert ya tashi, inda nan da nan ya sheka ofishin Yansanda a guje don ya kai musu rahoto, ba tare da bata lokaci ba kuwa Yansanda suka isa gidan.
Isar jami’an Yansanda keda wuya sai dai suka tarar da mutanen gaba daya sun fita hayyacinsu, cikin gaggawa suka garzaya dasu duka zuwa Asibiti, inda a can likitoci suka tabbatar da mutuwar mutane 6 daga cikinsu, yayin da sauran 23 suke cikin mawuyacin hali.
Sai dai kaakakin yace tuni kwamishinan Yansandan jahar, Rabiu Ladodo ya bayar da umarnin kaddamar da cikakken bincike domin gano gaskiyar lamarin, tunda acewarsa ba zasu dogara da rahoton Herbert ba.
Sai dai wasu majiyoyi daga garin Mbieri sun bayyana cewa mai yiwuwa bakin sun shaki hayakin na’urar wutar lantarki ta janaretan da aka kunna musu ne, sakamakon an girkeshi kusa da tagogin dakin da suka kwana don gudun barayi su yi awon gaba dashi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng