Zaratan Sojojin Najeriya sun halaka manyan kwamandojin Boko Haram 9 (Hotuna)

Zaratan Sojojin Najeriya sun halaka manyan kwamandojin Boko Haram 9 (Hotuna)

Kungiyar Boko Haram mai rajin kafa daular musulunci a yankin Afirka ta yamma, ISWAP, ta tabbatar da mutuwar wasu manyan kwamandojinta dake magana da yawunta guda 9, inji rundunar sojojin kasa ta Najeriya.

Legit.ng ta ruwaito rundunar Sojan ta sanar da haka ne a shafinta na kafar sadarwar zamani ta Facebook da sanyin safiyar Litinin, inda ta bayyana cewa Boko Haram ta dade tana amfani da kafar sadarwar yanar gizo don watsa farfaganda da karairayi.

KU KARANTA: Buhari ya yi maraba da murabus din Alkalin Alkalai Onnoghen

Zaratan Sojojin Najeriya sun halaka manyan kwamandojin Boko Haram 9 (Hotuna)

Yan Boko Haram
Source: Facebook

Amma rundunar tace tun bayan da dakarunta suka halaka wasu manyan kwamandojin kungiyar masu magana da yawunta kungiyar ta daina watsa ire iren wannan farfaganda, wanda hakan ya tabbatar da ikirarin rundunar Soji na gurgunta Boko Haram.

Ga dai cikakken jerin sunayen kwamandojin na Boko Haram da Sojoji suka halaka kamar haka;

Abu al-Qa'qa' al-Maiduguri.

Abu Khubayb bin Ahmed al-Barnawi.

Abu Ali al-Bamawi.

Ahmed al-Muhajir.

Abu Musa al-Camerooni.

Abu Abdullah Ali al-Barnawi

Abu Musab Muhammed Mustafa al-Maiduguri.

Ali al-Ghalam al-Kajiri.

Abu Hurayra al-Barnawi.

Zaratan Sojojin Najeriya sun halaka manyan kwamandojin Boko Haram 9 (Hotuna)

Yan Boko Haram
Source: Facebook

A wani labarin kuma, Shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ya sadaukar da alawus din da zai samu na barin majalisa kacokan ga iyayen wasu mata uku da ayyukan ta’addanci na kungiyar yan ta’addan Boko Haram suka shafa.

Saraki ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuni, inda yace baya ga wadannan mata guda uku, Sanatan ya sadaukar da sauran kudin ga iyalan takwarorinsa Sanatoci da suka mutu domin amfanin abinda suka bari.

Wadanda zasu amfana da wannan tagomashi sun hada da iyayen Leah Sharibu, dalibar da Boko Haram ta sace daga makarantar yan mata dake garin Dapchi jahar Yobe, sai kuma iyayen Hussaina Ahmed da Hauwa Liman, jami’an bada agaji da Boko Haram suka kashesu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel