Shugaba Buhari: Ni talaka ne kuma masoyana ma talakawa ne

Shugaba Buhari: Ni talaka ne kuma masoyana ma talakawa ne

-Shugaaba Buhari yace irin mutanen da ya ke gani lokacin yakin neman zabe yasan kudi ba zai iya sayen soyayyar su ba

- Ya ce har yanzu shi bashi da kudi, kuma yawancin masoyanshi suma talakawa ne

- Ya ce yaji dadi irin karfin gwiwar da ya dinga samu daga gurin talaka lokacin yakin neman zabe

Ranar Talatar nan da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, yayi magana akan zaben da ya gabata, wanda ya samu nasarar komawa a karo na biyu, inda ya bayyana cewa har yanzu yana jin dadin karfin gwiwar da ya samu a lokacin yakin neman zabe.

Shugaban kasar kuma yayi Allah wadai da mutanen da suke kiran kansu shugabanni, wanda suke amfani da wata dama suna jefa kasar nan cikin matsin rayuwa musamman ma a wannan yanayi da ake fama da matsalar tattalin arziki.

Yayi amfani da nasarar da ya samu a lokacin yakin neman zabe, inda yace karfin gwiwar da ya samu a gurin al'umma lokacin yakin neman zabe dinsa a kowacce jiha ita ce take kara masa jin dadi a zuciyarsa.

A cewar Buhari, sayen kuri'u ko amfani da kudin kasa ba zai iya sanyawa ya samu irin wannan jama'a ba.

KU KARANTA: An kama wani malamin makarantar Allo da ya ke hada kai da Almajiransa suna satar mutane

Buhari yayi wannan maganar ne a Abuja, lokacin da shirya karbar wasu baki da suka zo masa gaisuwar salla a fadarsa dake babban birnin tarayya Abuja.

Haka kuma da yake magana akan irin abinda ya fahimta lokacin zabe, Buhari yayi amfani da wannan damar ya tsokani Sanata Phillip Aduda, wanda yake dan jam'iyyar PDP, wanda ya zauna a hannun daman shugaban kasar.

Ya ce duk da cewa mutanen birnin Abuja basu zabe shi ba, amma hakan ba zai hana yayi musu adalci a mulkin shi ba. Sai dai kuma yace zai kare kanshi da mataimakinsa daga gare su saboda yana ganin Masharranta ne su shine yasa basu zabe shi ba.

"Naji dadi sosai da 'yan Najeriya suka fahimce ni, duk da cewa nayi ministan man fetur, sannan kuma nayi shugaban kasa a lokacin mulkin soja, mutane sun san cewa ba kudi ne dani ba, ballantana na basu.

"Kowa yasan cewa yawancin masoyana basu da abincin yau ballanatana na gobe, dole sai sun fita sun nemo, kuma ni bani da kudin da zan basu. A shekarar 2011 mun dogara ga Allah, a shekarar 2015 sai Allah ya kawo fasahar sake yanayin kada kuri'a na PVC, kuma cikin ikon Allah muka lashe zabe," in ji shugaba Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel