Jerin sunaye: Majalisar dokokin jihar Sokoto ta tabbatar da kwamishinoni 26 da Tambuwal ya aika da sunan su

Jerin sunaye: Majalisar dokokin jihar Sokoto ta tabbatar da kwamishinoni 26 da Tambuwal ya aika da sunan su

Majalisar dokokin jihar Sokoto ta tabbatar da sunayen mutane 26 a matsayin kwamishinoni bayan gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal, ya aika da sunayensu.

Tambuwal, wanda ya yi takara a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, ya zama gwamnan jihar Sokoto a karo na biyu bayan ya kayar da dan takarar jam'iyyar APC, Alhaji Ahmad Aliyu, a zaben 2019 da banbancin kuri'u 342 kacal.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar zangon wa'adin mambobin majalisar dokokin jihar za kare a sati mai zuwa.

Majalisar dokokin da zata karba daga hannun wannan na da mabobi 30; jam'iyyar PDP na da mambobi 14 yayin da APC ke da mambobi 16.

Majalisar ta tabbatar da sunayen mutanen da Tambuwal ya nada ne bayan shugaban masu rinjaye a majalisar, Alhaji Garba Bello, ya gabatar da kudirin neman yin a hakan a zauren majalisar.

Jerin sunaye: Majalisar dokokin jihar Sokoto ta tabbatar da kwamishinoni 26 da Tambuwal ya aika da sunan su

Aminu Waziri Tambuwal
Source: Twitter

"Gwamna Aminu Tambuwal ya aiko da sunayen mutane 26 da yake son bawa mukamin kwamishina domin wannan majalisa ta tabbatar da su.

"Dukkan sunayen da ya aiko, sunayen mutane ne masu mutunci da ke da gogewar aiki daga matakan da suka taka a baya kuma yanzu a shirye suke domin taimaka wa gwamna domin ya sauke nauyin da ke wuyansa," a cewar sa.

Bayan ya fadi hakan ne sai ya bukaci mambobin majalisar su kasu zuwa kananun kwamitoci domin gaggauta tantance mutanen da gwamnan ya aiko.

Bayan hakan ne sai mataimakin shugaban majalisar, wanda ya jagoranci zaman majalisar na ranar Alhamis, ya sanar da cewar majalisar ta tabbatar da dukkan sunayen mutane 26 da Tambuwal ya aiko a matsayin kwamishinoni a jihar Sokoto.

DUBA WANNAN: Gwamnatin Buhari ta kwace rijiyoyin man fetur 6 daga hannun kamfanoni 5

NAN ta rawaito cewar daga cikin mutanen da suka samu mukamin kwamishinan akwai Alhaji Salihu Maidaji, wanda shine shugaban majalisar dokokin jihar Sokoto ta yanzu kuma da ga tsohon gwamnan jihar Attahiru Bafarawa da kuma Alhaji Abdussamad Dasuki, mamba a majalisar daga mazabar Tambuwal/Kebbe.

Tsohon sakataren gwamnatin jihar Sokoto, Farfesa Bashir Garba, mamba a majalisar dokokin jihar da ya sha kaye a hannun jam'iyyar APC, Dakta Balarabe Kakale, da tsohon mamba a majalisar wakilai, ALhaji Umar Bature da Arzika Tureta na daga cikin sabbin kwamishinonin.

Ragowar sun hada da Abdullahi Maigwandu, Kanal Garba Moyi (mai ritaya), Farfesa Aisha Madawaki, Sulaiman Usman (SAN) da Kulu Haruna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel