Tsiyar yan NEPA: Mutane 350,000 zasu koma rayuwa a cikin duhu a jahar Kano

Tsiyar yan NEPA: Mutane 350,000 zasu koma rayuwa a cikin duhu a jahar Kano

Kamfanin dake rarraba wutar lantarki a jahohin Kano, Katsina da Jigawa ta kaddamar da aikin yankan wuta a jahar Kano na babu sani babu sabu kuma babu kakkautawa, inda ta dauki alwashin yanke ma gidaje dubu dari uku da hamsin wuta.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kamfanin KEDCO zata fara wannan aiki ne da rukunin gidaje da kamfanoni na farko da basa biyan kudin wuta, wanda adadinsu ya kai dubu tara, (9,000), inda zuwa yanzu, kwanaki biyu da fara aikin ta yanke ma mutane 2,300 wuta.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Ganduje ya fara shirin tsige Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II

Sai dai wasu ma’abota amfanin da wutar lantarkin sun bayyana bacin ransu da KEDCO, inda suka ce wannan zalunci ne tsagwaronsa, inda wani yace “akan me za’a yanke wuta a yanzu da ba’a samun wutar

“Sai kaga karamin gida suna bashi kudin wuta N10,000 zuwa N15,000, alhali idan aka duba masu gidan ko dutse guga basu dashi, balle butar lantarki, ta yaya suka sha wutar data kai wannan makudan?” Inji shi.

Shi kuma wani mazaunin garin Kano cewa yayi “Idan har da gaske KEDCO suke yi kamata yayi su samar da mitocin wuta a kowanne gida kamar yadda gwamnatin tarayya ta umarcesu, kaga kenan iya abinda ka siya iya abinda zaka sha kenan.”

Shima shugaban sashin tattara kudade na KEDCO, Johnson Adedeji ya tabbatar da kaddamar da wannan aiki na yankan wuta, inda yace daga faraway sun yanke na gidaje 2,300, ya kara da cewa sun gano akwai gidaje 350,000 da basu biya kudin wuta a cikin watanni 6 da suka gabata ba.

Sai dai yace tun bayan fara aikin yankan wutar, mutane da dama sun fara zuwa ofishinsu suna rage basussukan da kamfanin wutar ke binsu, basussukan da yace jimillansu sun kai naira biliyan 139.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng