Boko Haram: Gwamna Zulum ya kara wa dakarun sa kai alawus a jihar Borno

Boko Haram: Gwamna Zulum ya kara wa dakarun sa kai alawus a jihar Borno

Sabon gwamnan jihar Zamfara Babagana Zulum, a ranar Larabar da ta gabata ya bayar da sanarwar kara wa dakarun sa kai albashin su daga Naira dubu goma sha biyar zuwa dubu ashirin a kowane wata.

Gwamnan yayin bayar da wannan sanarwa ya ce karin albashin na zuwa ne duba da yadda dakarun sa kai da kuma mafarauta ke taka muhimmiyar rawar gani a fagen agazawa kwazon hukumomin tsaro wajen ci gaba da yakar kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.

Ana iya tuna cewa tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, shi ne ke da alhakin assasa kungiyar dakarun sa kai CJTF da babbar manufa ta bayar da muhimmiyar gudunmuwa da kuma tallafi wajen ci gaba da yakar ta'addanci a jihar.

Yayin isar da wannan sako ga mambobin kungiyar dakarun sa kai da kuma mafarauta a babban dakin taro na fadar gwamnatin sa dake birnin Maiduguri, gwamna Zulum ya yabawa kwazon su a fagen yaki da ta'addanci.

KARANTA KUMA: Takun da Buhari ya kamata ya sauya a wa'adin sa na biyu - Lauyoyin Najeriya

Kazalika gwamna Zulum ya gana da rundunonin 'yan sanda, hukumar DSS, da kuma kwamandun dakarun soji inda ya jaddada muhimmancin hadin kai a tsakanin su da kungiyar dakarun sa kai da kuma mafarauta wajen kawo karshen ta'addancin Boko Haram.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel