Hawan Sallah: Rikicin yan sara suka ya barke, an kashe mutum 1, 14 sun samu rauni

Hawan Sallah: Rikicin yan sara suka ya barke, an kashe mutum 1, 14 sun samu rauni

Rundunar Yansandan jahar Bauchi ta tabbatar da mutuwar mutum daya tare da samun rauni na mutane goma sha hudu a sanadiyyar wata rikici data barke a tsakanin wasu kungiyoyin sara suka da suka dade suna gaba da juna.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan rikici dai ya barke ne a washegarin sallah, daidai lokacin da ake gudanar hawan Sallah a garin Bauchi, guda daga cikin shagulgulan da ake gudanarwa don bayyana farin ciki tare da murnar zagayowar ranar Sallah.

KU KARANTA: Duka biyu: Gobara ta cinye kayan tallafin yan gudun hijira a jahar Borno

Cikin wata sanarwa da Kaakakin Yansanda, DSP Kamal Datti ya bayyana, yace lamarin ya auku ne da misalin karfe 11:30 na safiyar Laraba, 5 ga watan Yuni a yayin hawa lokacin da Sarkin Bauchi yake kan hanyarsa ta zuwa fadar gwamnati don gaishe da gwamnan jahar.

“Da misalin karfe 11:30 na safe yayin da ake gudanar da hawan Sallah, wasu gungun mafarauta dake cikin tawagar hakimin Darazo da hakimin Duguri sun baiwa hammata iska tare da amfani da makamai.

“A dalilin haka wani matashi daga garin Darazo, Auwalu Sadau ya rasa ransa a sanadiyyar harbin bindigar toka daya sha, yayin da wasu mutane goma sha hudu suka samu rauni, kuma a yanzu suna samun kulawa a asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi.

“Amma a sakamakon sanin makaman aiki da kuma kwarewa, ba tare da bata lokaci ba rundunar Yansanda ta shiga aikinta, inda cikin kankanin lokaci muka kama mutane 55, adduna 46, takubba 13, wukake 15, gorori 13 da bindigar toka 1, zuwa yanzu hankula sun kwanta a yankin.” Inji shi.

Daga karshe kaakaki Kamal Datti yace tuni rundunar ta kaddamar da binciken kwakwaf don gano musabbabin rikicin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel