Azumi 6 na watan shawwal bidi’a ne a fahimtar Imamu Malik – Inji Sheikh Ahmad Gumi
Shahararren Malamin addinin Islama dake garin Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya bayyana cewa azumin guda shida da Musulmai ke yi bayan kammala azumin watan Ramadana, a cikin watan Shawwal bai inganta ba, kuma bidi’a ne.
Gumi ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo daya watsa a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook a ranar Laraba, 5 ga watan Yuni, inda yace a fahimtar babban Malamin addinin Musulunci, Imamu Malik, Azumin Sittu Shawwal bai inganta ba, sahabbai, tabi’ai, duk basu yi ba
KU KARANTA: Sarkin Kano ya musanta zargin almubazzarantar da naira biliyan 3.4
Legit.ng ta ruwaito Sheikh Ahmad Gumi ya karanto ruwayar wani magabaci da ake kira Yahaya wanda yace “Naji Malik yana maganan yin azumin sittatin na bayan an bude baki, yace bai taba ganin ma’abota ilimi da fikihu sun yi azumin ba.
“Kuma bai taba ganin magabata nagari sun yi ba, hakazalika ma’abota ilimi sun karhanta azumi 6 na bayan Ramadan, har ma suna tsoron zai iya zama bidi’a saboda bashi da asali a cikin addini” Inji shi.
A cigaba da jawabinsa, Sheikh Gumi ya bayyana cewa, uwar muminai, matar Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, Aisha, bata rama azumin watan Ramadan sai a watan sha’aban ma, ma’ana da azumin shawwal ya inganta da an ruwaito tayi.
Bugu da kari Gumi ya bayyana ma masu fahimtar sahihancin hadisin dake kira ga azumin sitta shawwal cewa Malik ya san hadisin, kuma Malik a garin Madina ya rayu kafin Annabi ya cika shekaru 150 da mutuwa, don haka ya san hadisin, amma hadisin bai inganta ba.
Daga karshe Malamin ya bayyana cewa akwai raini ga Imamu Malik cikin kiran mutane su yi azumin sitta Shawwal, saboda dama a ko ina akwai masu da’a da bin nagaba da kuma masu yin bore ga nagaba.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng