Budurwa ta mari saurayinta sau 52 saboda ya gaza siya mata wayan salula

Budurwa ta mari saurayinta sau 52 saboda ya gaza siya mata wayan salula

- Wata budurwa ta yiwa saurayinta duka a fili saboda ya gaza siya mata wayan salula

- Saurayin ya kare budurwarsa yayin da 'yan sanda suka iso inda lamarin ke faruwa

- Ya shaidawa 'yan sandan cewa ya kyalle ta ta doke shi ne domin hakan zai sanyaya mata rai

Bisa ga dukkan alamu shagulgulan ranar masoya na kasar China bai yiwa wasu dadi ba sakamakon mari da wata budurwa ta rika shararawa saurayinta saboda bacin rai na rashin siya mata sabon waya da saurayin bai yi ba.

Budurwa ta mari saurayinta sau 52 saboda ya gaza siya mata wayan salula

Budurwa ta mari saurayinta sau 52 saboda ya gaza siya mata wayan salula
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Sojoji sun tafka ma 'yan Boko Haram mummunan asara a Abaganaram

Na'urar daukan bidiyo na sirri da kuma wasu mutane sun nade faifan bidiyon da ya nuna wata mata a garin Dazhou tana dukkan saurayin ta har da mari a fuskansa yayin da shi kuma ya tsaya bai kare kansa ba.

A yayin da 'yan sanda suka iso wurin da lamarin ke faruwa, saurayin ya yi yunkuri kare budurwarsa duk da cewa ba ta dena dukkansa ba inda ya shaidawa 'yan sandan cewa za ta huce fushinta idan ta duke shi kamar yaddda wani kafar yadda labarai na Intanet mai sune The Cover ya ruwaito.

Binciken da 'yan sandan su kayi ya nuna cewar budurwar ta mare saurayinta sau 52 a bainar Jama'a. Wannan lamarin ya faru ne a ranar 20 ga watan Mayu ranar da ake bikin ranar masoya da tayi kama da ranar Valentine da ake yi a wasu kasashen duniya.

Daga bisani jami'an 'yan sandan sun sulhunta masoyan biyu a titin bayan sunyi alkawarin ba za su sake maimaita hakan ba a gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel