Ali ya ga Ali: Sarkin Kano Sanusi ya hadu da Ganduje a masallacin idi bayan ya ja shi Sallah (hoto)

Ali ya ga Ali: Sarkin Kano Sanusi ya hadu da Ganduje a masallacin idi bayan ya ja shi Sallah (hoto)

A yau Talata, 4 ga watan Yuni ne daukacin al’umman Musulmi a sassa daban-daban na duniya suka gudanar da bikin Eid-el Fitr bayan kammala azumin watan Ramadana.

Jama’a sun tunkari masallatai daban-daban domin cika ibadunsu na Ramadana ta hanyar godiya ga Allah madaukakin Sarki.

Hakan ce ta kasance a jihar Kano inda Sarakuna, manyan yan kasuwa, manyan yan siyasa ciki harda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje suka halarci Sallar idi.

Sarki Muhammadu Sanusi II ne ya jagoranci bayar da sallar idi a babban masallacin idi da ke Kofar Mata a Kano.

Bayan sun idar da Sallah an gano Gwamna Ganduje tare da Sarkin Kano suna Musabaha cike da farin ciki da walwala.

Ali ya ga Ali: Sarkin Kano Sanusi ya hadu da Ganduje a masallacin idi bayan ya ja shi Sallah (hoto)
Ali ya ga Ali: Sarkin Kano Sanusi ya hadu da Ganduje a masallacin idi bayan ya ja shi Sallah (hoto)
Asali: Twitter

Wannan shine karo na farko da shugabannin ke haduwa tun bayan kunnowar rikicin masarautar jihar, inda gwamnan ya kacaccala ta zuwa gida biyar.

KU KARANTA KUMA: Buhari yayi sallar idi a masallacin sansanin Mabilla da ke Abuja (hotuna)

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Fadar mai martaba sarkin Kano ta musanta zargin da hukumar yaki da rashawa da sauraron koke koken jama’a ta jahar Kano keyi mata tare da mai martaba Sarki Muhammadu Sunusi II na yin bindiga tare da almubazzarantar da naira biliyan 3.4.

Legit.ng ta ruwaito walin Kano, Alhaji Mahe Bashir ne ya bada wannan kariya ga masarautar a ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, inda yace zarge zargen da ake yi ma masarautar basu da tushe balle makama, sa’annan ya bayyana daki daki yadda masarautar ta kashe kudadenta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel