Shekau ya bayyana a sabon bidiyo, ya rera wakar taken Najeriya

Shekau ya bayyana a sabon bidiyo, ya rera wakar taken Najeriya

Shugaban kungiyar Jama'atu Ahlil-Sunnah Lid-Da'awati Wal-Jihad wacce aka fi sani da Boko Haram, Abubakar Shekau, ya bayyana sanye da fararen kaya a cikin wani sabon faifan bidiyo da ya fitar.

A cikin faifan bidiyon, shekau ya karanta akidun kungiyar Boko Haram a cikin harshen Larabci yayin da yake rike da babbar bindiga samfurin AK47.

Shekau ya samu rauni a matsayinsa na shugaban kungiyar Boko Haram bayan kungiyar ta rabe gida biyu a shekarar 2016 da kuma ragargazar mayakansa da rundunar sojojin Najeriya da na hadin gwuiwar kasashen gefen tekun Chadi ke yi.

Shekau ya yi ta kokarin karanta akidun kungiyar Boko Haram cikin harshen Larabci a lokaci guda kuma yana cakuda wa da rera wakar taken Najeriya (National Anthem), wanda ya sha nanata cewar yin sa Shirka ce.

Shekau ya bayyana a sabon bidiyo, ya rera wakar taken Najeriya
Shekau a sabon bidiyo
Asali: Twitter

Shekau ya bayyana a sabon bidiyo, ya rera wakar taken Najeriya
Shekau ya bayyana a sabon bidiyo
Asali: Twitter

Wani mai nazarin harkokin kungiyoyin ta'addanci ya bayyana cewar Shekau ya fitar da faifan bidiyon mai tsawom minti 35 ne domin aika sako ga kungiyoyin ta'addanci na kasa da kasa biyo bayan rikicin shugabanci da kungiyar ke fama da shi a yankin kasashen gefen tekun Chadi.

DUBA WANNAN: Biyu babu: APC ta kori tsohon gwamna Yari daga jam'iyyar

Ragowar kungiyoyin da suka balle daga jikin Boko Haram na sukar tsatstsauran ra'ayi da akidun Shekau, musamman amfani da mata da kananan yara a matsayin 'yan kunar bakin wake a wuraren ibadar Musulmi, sansanin 'yan gudun hijira, kasuwanni da sauran wuraren taruwar jama'a.

A cewar mai hasashen, Shekau ya fitar da faifan bidiyon ne domin neman irin taimakon da ragowar tsagin kungiyar ke amfana daga kungiyoyin dake daukan aiyukan ta'addancin da suke tafka wa a kasashen gefen tekun Chadi.

Alamu na nuna cewar Shekau ya samu matsalar ido saboda yadda yake ta in-ina wajen karanta takardar rubutaccen jawabin da ya yi ta kokarin ya karanta cikin harshen larabci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng