Buhari ya gana da Abdulsalamu a Saudiyya, zai dawo gida Najeriya a yau
Tsohon shugabar kasar Najeriya a mulki soji, Abdulsalamu Abubakar, ya ziyarci shugaba Buhari a kasar Saudiyya domin gana wa ta musamman. Babu wata sanarwa ko bayani a kan dalilin ganawar shugabannnin biyu a kasar Saudiyya. Shugaba yana kasar Saudiyya ne domin halartar taron kasashen Musulmi na OIC.
Da yammacin ranar Lahadi (yau) ne ake sa ran shugaba Buhari zai dawo gida Najeriya bayan kammala taron da ya halarta.
A yayin taron na OIC da ya halarta, shugaba Buhari ya jinjina wa kungiyar kasashen OIC na bayar da gudunmawa wajen sake jawo ruwa domin farfado da tekun Chadi.
DUBA WANNAN: Fashi da garkuwa da mutane: Sojoji Sun kama rikakkun 'yan ta'adda 5 a Katsina (Hotuna)
Tuni sanarwa ta fita cewar shugaba Buhari zai karbi bakuncin shugabannin kasashen gefen tekun Chadi kwanaki kadan bayan dawowarsa daga kasar Saudiyya. Ana tunanin taron ba zai rasa nabasa da gudunmawar da kungiyar kasashen OIC zata bayar ba wajen farfado da tekun Chadi.
A kwanakin baya ne babban sakataren majalisar dinkin duniya, Antoni Guterres, ya nada shugaba Buhari a matsayin wanda zai zama shugaba na biyu a kwamitin neman hada kudaden da za ai amfani da su domin farfado da tekun Chadi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng