Jerin gwamnonin da suka shafe fiye da shekaru takwas akan mulki

Jerin gwamnonin da suka shafe fiye da shekaru takwas akan mulki

Ga wasu gwamnoni guda uku da majiyarmu ta binciko muku da suka shafe sama da shekaru takwas suna more kujerar mulki a jihohin su

Tsarin kundin mulkin Najeriya ya yarda gwamnoni suyi wa'adi sau biyu ne kawai, ko wanne wa'adi zasu yi shekara hudu a kan mulki, ya zama shekaru takwas kenan duka idan aka hada. A wannan rahoton majiyarmu Legit.ng za ta kawo muku jerin wasu gwamnoni guda uku da suka yi fiye da shekaru takwas akan mulki, da kuma dalilan da yasa suke yi wadannan shekarun.

Jerin gwamnonin da suka shafe fiye da shekaru takwas akan mulki

Jerin gwamnonin da suka shafe fiye da shekaru takwas akan mulki
Source: Facebook

Rev. Jolly Tavoro Nyame

Duk da dai yanzu haka yana gidan kurkuku, tsohon gwamnan Taraba, Jolly Nyame yana daya daga cikin gwamnonin da suka shafe sama da shekaru takwas akan kujerar gwamna.

Ya shiga harkar siyasa a shekarar 1991, inda ya fito takarar gwamna a watan Janairun shekarar 1992, ya kuma samu nasara. Sai dai kuma ya samu matsala, a lokacin da Marigayi Janar Sani Abacha ya kwace mulki daga hannun Ernest Shonekan.

Abacha ya kwace mulkin a watan Nuwamba, 1993, inda ya nada sojoji a matsayin gwamnoni suka karbe kujerun a hannun Nyame da sauran gwamnoni 'yan uwanshi.

Bayan shekaru shida, Nyame ya sake fitowa takara a shekarar 1999, a jam'iyyar PDP kuma ya sake lashewa. Bayan ya shafe shekaru hudu akan kujerar gwamnan jihar, an sake zabar shi a shekarar 2003, hakan ya sanya ya zama mutum na farko da ya lashe zaben gwamna sau uku a jihar Taraba.

Engr. Bukar Abba Ibrahim

Labarin gwamna Bukar Abba Ibrahim, iri daya ne dana Jolly Nyame, Sai dai shi kuma Bukar Abba Ibrahim bayan ya lashe kujerar gwamna sau uku a jihar Yobe, ya kuma samu damar lashe kujerar Sanata sau uku a jihar.

KU KARANTA: Wadanda suka sace ni sunce suna nan suna farautar Shugaba Buhari da Atiku Abubakar - Salisu Mu'azu

Ibrahim Gaidam

Sai dai shi kuma Ibrahim Gaidam labarin nashi ba iri daya bane dana Jolly Nyame da Bukar Abba.

Ba kamar Nyame da Bukar ba wadanda suka lashe zabe sau uku a lokaci daya. Gaidam ya lashe zaben gwamna sau biyu ne kawai, amma ya samu damar yin gwamna a karo na uku bayan faruwar wani lamari.

Gaidam shine gwamnan jihar Yobe na yanzu da ya bar mulki, bayan ya shafe shekaru goma akan kujerar gwamnan jihar. Ya zama gwamnan jihar a karo na farko ne bayan mutuwar tsohon gwamnan jihar, Mamman Ali, a shekarar 2009.

Kafin 2009, a watan Afrilu 2007, an zabi Gaidam a matsayin mataimakin gwamnan jihar Yobe a karkashin jam'iyyar ANPP, inda aka rantsar dasu ranar 29 ga watan Mayu, 2007.

Sannan kuma an rantsar dashi a matsayin gwamnan jihar a ranar 27 ga watan Janairu, 2009 bayan rasuwar gwamnan jihar Mamman Ali, a birnin Florida dake kasar Amurka. Abubakar Ali, dan uwan Mamman Ali shine ya zama sabon mataimakin gwamnan jihar.

Bayan ya kammala shekaru hudun da maigidansa ya fara, an sake zabar Gaidam a ranar 26 ga watan Afrilu, 2011, a matsayin gwamnan jihar a karo na biyu. Sannan an sake zabar shi a ranar 11 ga watan Afrilu, 2015, a matsayin gwamnan jihar karo na uku, wanda ya kammala mulkin shi ranar 28 ga watan Mayun wannan shekarar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel