Mijina yana saduwa da wata mahaukaciya - Wata mata ta nemi kotu ta raba aurensu

Mijina yana saduwa da wata mahaukaciya - Wata mata ta nemi kotu ta raba aurensu

- Wata mata ta kai mijinta kara da bukatar kotu ta raba aurensu wanda suka shafe shekaru 14 suna tare

- Matar ta kai karar ne saboda tana zargin mijin nata yana kwanciya da mahaukaciya

- Bayan haka kuma mijin nata yana yawan yi mata barazanar kisa a lokuta da dama

Jiya Juma'a ne wata kotu a garin Ado-Ekiti ta raba wasu ma'aurata da suka shafe shekaru 14 suna tare, masu suna Amaka Nwafor mai shekaru 36, da mijinta, Friday Nwafor mai shekaru 47 a duniya.

Alkalin kotun, mai shari'a Olayinka Akomolede, a rahoton da muka samu daga kamfanin dillancin labarai na Najeriya, ya raba auren ne sanadiyyar rikici da koda yaushe ma'auratan suke ciki, wanda ya hada da duka, cin zarafi, barazanar kisa da matar take samu daga wurin mijin.

Alkalin, ta kuma gano cewa auren ya riga ya ruguje saboda babu wani mutunci tsakanin mata da mijin.

Alkalin ta yanke hukuncin, matar ta cigaba da rike 'ya'yansu guda hudu, amma da sharadin duk wata mijin zai dinga aika musu da naira dubu biyu kowanne a matsayin kudin abinci. Sannan kuma kotun ta bai wa mijin damar zuwa ya gana da 'ya'yansa a duk lokacin da yake bukata.

Amaka ta bayyanawa kotu cewa mijinta yana zarginta da cewa tana zuwa gurin wani mutumi. Ta bayyana cewa gaskiya ne tana zuwa gurin mutumin, sai dai kuma tace mijin nata ne ya sanyaa ta cikin wannan halin, saboda baya kula da ita.

Sannan kuma Amaka ta yi zargin cewa mijin nata shi kuma yana zuwa ya kwanta da wata mahaukaciya.

KU KARANTA: 'Yan Shi'a sun sanyawa tutocin kasar Amurka da ta Isra'ila wuta a Abuja

Ta kuma bayyana cewa mijin nata ya sha yi mata barazanar kisa, ta kara da cewa a lokuta da dama da yake yi mata barazanar zai dauko 'yan daba ya biyasu naira dubu biyar domin su kasheta.

Sai dai kuma mijin ya musanta wadannan zargi da matarshi take yi masa, inda ya bayyana cewa duka ta kirkire su ne.

Friday ya bayyana matar tasa a matsayin mazinaciya, inda ya kara da cewa ta sha barin gidansa ta tafi gidan wani mutumi ta shafe kwana uku suna tare.

A karshe yace a shirye yake yaga an raba auren, domin shima dama ya gaji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng